BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Za a yi wa Conte tiyata a matsarmama

Antonio Conte

Wed, 1 Feb 2023 Source: BBC

Za a yi wa kocin Tottenham Antonio Conte tiyata a matsarmamarsa.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta tabbatar cewa za a iya masa aiki tare da cireta yau Laraba.

An gano cewa kocin dan kasar Italiya mai shekaru 53 na fama da kumburin matsarmamar, bayan da ya yi fama da ciwon ciki.

Wasan Spurs na gaba za ta kara ne a gida da Manchester City a gasar Premier League ranar Lahadi.

Sanarwar kungiyar ta ce zai dawo bakin aiki da zarar ya warke.

A yanzu kungiyar da Conte ke horarwar na zaune ne a na biyar da maki 36, maki 14 tsakaninsu da abokan hamayyarsu Arsenal da ke kan teburi.

Jiya ne Tottenham ta kammala cinikin Pedro Porro daga Sportin Lisbon.

Source: BBC