Menu

Zaɓen 2023: Zarge-zargen da ake yi wa manyan 'yan takarar shugaban Najeriya

32410536 Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi

Tue, 17 Jan 2023 Source: BBC

Gabanin zaɓen 2023 da ke tafe ‘yan Najeriya na shirin zaɓar shugaban ƙasa daga cikin ‘yan takara 18, sai dai ‘yan takara na gaba-gaba guda uku da ake hasashen za su kai ga nasara, an sha zarginsu kan abubuwa da dama kama daga sana’ar sayar da ƙwayoyi da safarar kuɗaɗe da kuma ƙin biyan kuɗin haraji.

Sai dai ba a taɓa kama ko da ɗaya daga cikinsu ba da laifi ba, wanda kuma zai iya hana su yin takara, amma zarge-zargen da akeyi musu ya sanya musu faɗuwar daraja a idon ‘yan ƙasa.

"Zaɓe ne tsakanin gurɓatattun ‘yan takaru,’’ a cewar Auwal Musa Rafsanjani, shugaban gamayyar ƙungiyoyi masu sa ido kan zaɓe da siyasa, inda ya yi nuni kan irin rashin ci gaba da kuma talauci da ya dabaibaye Najeriya saboda cin hanci da rashawa.

Manyan ‘yan takarar kujerar shugaban ƙasar sun haɗar da Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar Labour.

Dukkansu uku sun ce sun samu arzikinsu ta hanya mai kyau.   

Takardun bayanai na Tinubu

Mista Bola Tinubu, wanda ya mulki jihar Legas sau biyu, shi ne ɗan takara da aka fi magana a kansa gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Sai dai muhawara ta ƙi ƙarewa kan ainihin shekarunsa da sunansa da batun lafiyarsa da irin aikinsa da kuma gaskiyar shaidarsa ta kammala karatun Jami’a, amma an fi magana kan batun lafiyarsa, inda mutane da dama ke ganin ba shi da ƙoshin lafiya da zai mulki ƙasar.

Mutane da dama na ganin Tinubu a matsayin ɗaya daga cikin hamshaƙan 'yan siyasa a Najeriya duk da cewa babu bayanai da suka tabbatar da hakan.

An yi ta magana kan batun arzikinsa ne a zaɓen 2019, lokacin da mutane suka ga wasu manyan motoci biyu daga banki cike da kuɗi suka shiga gidansa mai bene a anguwar Ikoyi da ke Legas.

Sai dai masu taimaka masa sun musanta zargin cewa yana da hannu kan batun sayan ƙuri’a.

A watan Disamba, ya faɗa wa BBC cewa ya gaji sana’ar sayar da gidaje wanda daga baya ya ƙara zuba kuɗi a harkar, sai dai, a baya ya ce ya zama babban miloniya ne lokacin da yake matsayin mai binciken kuɗi a kamfanin Deloitte and Touche.

Ya ce ya tara kusan dala miliyan 1.8 daga albashinsa da kuma alawus-alawus a wannan aiki, wanda kuma hakan aka samu cikin asusunsa a wani bincike da hukumomin Amurka suka yi kansa a shekarar 1993.

A wasu takardu marasa kyau da suka fito bainar jama’a, sashin ma’aikatar shari’a na Amurka sun yi zargin cewa daga 1988, asusun banki da aka buɗe da sunan Bola Ahmed Tinubu, yana dauke da kuɗaɗen kwaya, abu kuma da aka haramta sayarwa a ƙasar.

Jami’i na musamman da ya gudanar da binciken, Kevin Moss, ya ce mista Tinubu ya yi aiki da wanda suke zargi Adegoboyega Akande.

Jami’in ya ce Tinubu ya faɗa masa ta wayar tarho cewa ya san mista Akande, sai dai daga baya ya yi amai ya lashe, inda ya ce babu alakar kuɗi tsakaninsa da mutumin.

A daidai lokacin da kotu ta yi imanin cewa kuɗin da aka samu daga asusun suna da alaƙa da safarar ƙwayoyi, mista Tinubu da wasu sun amince da aikata laifi, amma kotu ba ta yanke hukuncin ƙarshe ba na cewa kuɗin na safarar ƙwayoyi ne.

Maimakon haka ne ma Tinubu ya cimma yarjejeniyar kuɗi da hukumomi, inda ya rasa dala 460,000.  

Tinubu ya sha musanta kansa da alaƙa da masu sana’ar ƙwayoyi, inda mai magana da yawunsa Festus Keyamo, ya ce kuɗaɗen da maigida nasa ya rasa, ya rasa su ne ba wai kan zargin aikata laifi ba.

Ana kallon Tinubu mai shekara 70 a matsayin kwararren ɗan siyasa, kuma wannan na cikin abubuwa da ake zarginsa.

A shekara da ya gabata, ya cimma wata yarjejeniya ta bayan kotu da Akanta Oladapo Apara, bayan samun saɓani tsakaninsu.

Mista Apara, shi ne mamallakin kamfanin Alpha Beta Consulting, wanda aka kirkiro  lokacin da Tinubu yake gwamna a jihar Legas, inda ya ba shi manyan kwangiloli na haraji karbo haraji jihar, wanda kamfanin ke rike da shi.  

Akpara ya yi zargin cewa Tinubu na da kashi 70 na kuɗaɗen shiga da kamfanin ke samu – inda kamfanin ya samu sama da ladan kashi 10 na kuɗin da aka karɓa, da aka kiyasta zai kai dala miliya 3.48 tsakanin shekarar 2002 zuwa 2018.

An kori Akpara a kamfanin a shekarar 2010 bayan gano cewa an yi sama da faɗi da wasu kuɗaɗe – inda aka shigar da shi ƙara domin karɓo wasu kuɗaɗe.

Ya ƙalubalanci cewa ba a da hurumin korarsa a matsayinsa na shugaban kamfanin, inda ya nemi diyya daga wajen Tinubu, wanda ya kai su ga kotu a 2021.

A watan Satumban 2018, ya wallafa a shafinsa na Tuwita cewa ya rubuta wa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya wasiƙa, inda ya zargi kamfanin Alpha Beta da ƙin biyan kuɗin haraji – amma ya ce tuni aka goge rubutun a shafin nasa.

Kamfanin Alpha Beta dai ya musanta zargin, inda ya ce an kori mista Akpara saboda zargin almundahana, abu kuma da ya musanta.

Tinubu ya sha musanta zargin alaƙa da kamfanin Alpha Beta, inda ya ce baya samun kuɗin lada daga kuɗaɗen haraji da gwamnatin jihar Legas ke karɓa.

Sai dai, ya cimma wata yarjejeniyar biyan diyya da ba a bayyana ba da mista Akpara, wanda kuma ya kai ga janye ƙarar daga kotu.

Takardu da suka fito bainar jama’a kan yarjejeniyar, ya kunshi wani bangare inda Alpha Beta zai biya kuɗin da ake bin sa zuwa ga Akpara, in har Tinubu ya karya alkawarin da ya cimma.

Peter Obi da binciken Pandora

Peter Obi, wanda shi ma ya yi mulki har sau biyu a matsayin gwamna – idan aka koma kansa musamman a jiharsa ta Anambra, ba ɓoyayyen abu ba ne kan batun arzikin da ya mallaka, wanda ya ce ya samu ta hanyar haɗa-haɗar bankuna da shigo da kayayyaki cikin Najeriya.

Magoya bayansa na kiransa da ‘mai tsafta’ saboda kasancewarsa ɗan siyasar Najeriya da ba shi da zargin almubazzaranci da kuɗaɗen al’umma.

Sai dai abin ya zo wa mutane da dama da mamaki lokacin da saka bankaɗo sunansa a cikin takardun bincike na Pandora, wanda ya binciko takardu kusan miliyan 12 da suka nuna dukiya da aka ɓoye da wadanda suka ki biyan haraji da kuma safarar kuɗaɗe da wasu manyan masu arziki a duniya ke yi.

Takardun sun nuna cewa a shekarar 2010, lokacin da Peter Obi yake gwamnan Anambra, ya kirkiro da wani kamfani a wani tsibiri a ƙasar Birtaniya, da ya saka wa sunan ‘yarsa domin gudun biyan haraji.

Jaridar Premium Times ta Najeriya, da ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi binciken a 2021, ya nuna cewa mista Obi ya gaza bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada. An kuma gano cewa ya buɗe asussan banki da dama lokacin da yake ma’aikaci wanda kuma bai dace ba.

Binciken ya kuma bayyana cewa ya ƙi yin muraɓus daga kamfanin da ya kafa a Birtaniya, wanda ya kasance shi ne daraktan ta lokacin da ya hau mulki a Anambra – inda ya ci gaba da harkokin kasuwanci wadda kuma bai kamata ba a matsayinsa na babban jami’in gwamnati.

A martani da ya mayar kan zarge-zargen, Peter Obi, ya ce ba shi da masaniya cewa doka ta tanadi ya faɗi kadarorinsa da ya mallaka tare da iyalansa, inda ya ce ya miƙa ragamar harkokin ga matarsa, wacce ta kasance darakta, da kuma ya bai wa takardarsa ta murabus.

Ya ce bangaren rajista ya gaza sabunta canjin na tsawon watanni 14.

Ba a taɓa gurfanar da shi kan maganganun da ya yi.

An kuma zargi mista Obi mai shekara 61, na zuba jari da ya kai dala miliyan 20 a kamfanin sayar da giya a jihar sa wanda kuma iyalansa ke da hannun jari lokacin da yake gwamna.

Ya musanta zarge-zargen, inda ya ce zuba jarin da ya yi ya taimaka wa jihar Anambra ba ƙadan a cikin shekarun nan.

Atiku Abubakar da majalisar dattawan Amurka

Atiku Abubakar na kallon kansa a matsayin ƙwararren ɗan siyasa gabanin zaɓe da ke tafe, duba da cewa ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007 – wanda kuma lokaci ne da ya kasance mai cike da ce-ce-ku-ce.

Tsohon maigidansa, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya zarge shi da laifin almubazzaranci da kuɗin da ya kai dala miliyan 145, daga hukumar tallafin man fetur ta PTDF a 2003.

Obasanjo wanda ya kasance ba ya jin shakkar fitowa bainar jama’a ya bayyana ra’ayinsa, ya sadaukar da wani bangare na cikin takardarsa mai suna My Watch da aka wallafa a 2014, kan zarge-zargen da ake yi wa tsohon mataimakinsa.

Atiku Abubakar dai ya musanta zargin, inda ya ce an saka dala miliyan 145, a bankunan kasuwanci don samun riba ta yadda za a iya dawo da su cikin ayyukan PTDF.  

Ɗan siyasar mai shekara 76, ya ce silar arzikinsa ya faro ne daga harkar gonaki da mallakar gidaje a jiharsa ta Adamawa. Ya kuma ce ya yi aikin kwastam, inda tun farkon rayuwarsa ya samo dabarun neman kuɗi.

Ya ce a shekarun 1980, ya kafa wani kamfanin kula da harkar mai, inda ya samu kuɗaɗe da ya kasance cikin abubuwa da suka janyo masa samun arziki.

Sai dai masu adawa da shi , na zarginsa da yin watsi da dokar da ta haramta wa ma’aikatan gwamnati yin sana’o’i na kashin kansu ba ya ga noma.

A 2010, rahoton wani kwamitin majalisar dattawan Amurka, ya yi zargin cewa tsakanin shekarar 2000 zuwa 2008, Atiku ta hanyar ɗaya daga cikin matansa, ya tura kuɗi sama da dala miliyan 40 a wasu ‘assussa da ake zargi’ zuwa Amurka daga kamfanin mai na shell.

Rahoton ya ce akalla dala miliyan 1.7 na kuɗin ya zo ne daga cin hanci da wani kamfanin Jamus mai suna Siemens ya bayar, inda kuma ya amsa laifin bayar da na goro a kan zargin a 2008, da kuma amince ya biya tarar dala biliyan 1.6.

Source: BBC