Menu

'Za mu rufe bankuna ne saboda kare rayukan ma'aikatanmu'

85034291 Hoton alama

Thu, 9 Feb 2023 Source: BBC

Kungiyar ma’aikatan Bankuna da Insora ta Najeriya ta yi barazanar janye ‘yan kungiyar a daukacin fadin kasar sakamakon hare-hare da ake kai wa harabar wasu bankunan kasuwanci a kasar.

Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar karancin Naira wani abu da ke fusata masu hulda da bankunan.

Sakataren kungiyar na kasar Mohamamd Sheikh ya shaida wa BBC cewa " sakamakon fusatar da mutane suke yi sai su rinka kai wa ma'aikatanmu hari da duka da zagi da duk nau'in cin mutumci, muna tsoron ka da al'amarin ya wuce gona da iri da ka iya kai wa ga kisan kai ko wani abu makamancin hakan."

Ya kara da cewa "dole ne babban bankin kasar ya samar da isassun kudade ga bankuna, domin bankuna su bai wa jama'a idan kuma ba haka ba to za mu dauki matakin janye 'yan kungiyar tamu idan wa’adin da muka bayar na kwana bakwai ya cika don kare lafiya da rayuwarsu".

Mohammed Shaikh ya kara da cewa "idan har an ba mu kudaden da ake cewa babban bankin kasar yana ba mu to ina suke?"

Halin da ma'aikatan banki ke ciki

A yanzu dai da wuya ka samu wani ma'aikacin banki da ke sanye da kayan da ke nuna shi ma'aikacin banki ne.

"Mun umarce su da su rinka sanya kayan gida har zuwa lokacin da wannan al'amari zai kwanta domin muna gudun abin da zai iya samun su saboda yadda jama'a suka fusata", in ji wani babban jami'i a bankin Union Bank.

Jami'i na bankin Union wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa "mun rufe rassanmu kimanin 80 saboda hare-hare da ake kai musu. Akwai manajanmu ma da aka rufe shi da duka yana kan hanyarsa ta zuwa gida."

Ko a ranar Laraba bankin Zenith ya rufe ofisoshinsa a jihohin Legas da Delta, kana an hango wasu ma’aikatan bankin na neman haurawa ta katanga domin gudun haduwa da fushin abokan huldarsu da suka yi wa ofishinsu kofar rago.

Matakin ya tilasta wa ma’aikatan yin amfani da tsani suka haura kan katangar.

Wasu rassan bankin Zenith da ke Ikeja da Ikorodu da Agege ma dai sun kasance a rufe tun a jiya.

'Yan Najeriya sun fusata

'Yan Naijeriya dai na cewa tun bayan cikar wa’adin fara amfani da sabon kudi ta fara aiki ne babban bankin kasar ya rikewa harkokin kasuwancin kasar kurwarsu - wani abu da watakila zai jefa miliyoyin ‘yan kasar hali na ‘ya-kwance uwa-kwance.

Za dai a iya cewa tun lokacin da aka zo da sabon tsarin fasalin naira, bankunan suka sa mu kansu cikin hali na tsaka mai wuya.

Tun a farkon makon da ya gabata, an yi ta yada wasu faya-fayan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka nuna wani mutum tsirara na kuka tare da kira ga bankin su bashi kudinsa da yayi ajiya a wurinsu.

Haka kuma an hasko wata mata tana kada jiki irin na kauraye daga ita sai rigar nono a kirjinta da kuma wandon da take sanye da shi.

Source: BBC