BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Zan koma fim idan na yi ritaya daga dambe- Joshua

97061692 Anthony Joshua

Mon, 2 Jan 2023 Source: BBC

Dan wasan damben Burtaniya, Anthony Joshua ya ce zai koma fitowa a tauraron fina-finan Hollywood idan ya yi ritaya daga dambe.

Joshua wanda ya taba lashe kambun duniya har sau biyu, ya fada wa mujallar GQ ta Amurka cewa wasan dambe ya bude mashi hanyoyi da suka sa ya fara tunanin gwada wasan kwaikwayo.

''Ina so in gwada wani abu bayan dambe da nafi kwarewa a kansa,'' a cewar Joshua.

Ya kara da cewa '' Ina ganin bayan dambe zan koma fitowa a fina-finai saboda na yi talloli na ga yadda ake shirya su, kuma ba ni da matsala a gaban kyamara.''

Tauraruwar haifaffen Najeriyar ta yi kasa a baya-bayan nan, bayan da ya yi rashin nasara a dambensa da Olyksandr Usyk na Ukraine.

Source: BBC