Menu

Zlatan Ibrahimovic ya kafa tarihi a gasar Serie A

 117655512 Ibrahimovicmilan Zlatan Ibrahimovic

Mon, 22 Mar 2021 Source: BBC

Zlatan Ibrahimovic ya buga wa AC Milan gasar Serie A wasan mako na 28 da ta yi nasara a kan Fiorentina da ci 3-2 ranar Lahadi.

Da wannan sakamakon Milan ta rage tazarar maki tsakaninta da Inter wadda ke jan ragamar teburi, yanzu ya koma shida tsakaninsu.

Ibrahimovic ne ya fara ci wa Milan kwallo minti tara da take leda, kuma na 15 jumulla a bana, mai shekara 39 da kwana 169, shi ne wanda keda yawan shekaru da ya zura kwallo 15 a raga a kakar Serie A.

Wannan shi ne wasan farko da dan kwallon Sweden ya buga wa Milan, bayan jinya da ya yi tun raunin da ya ji ranar 28 ga watan Fabrairu a karawa da Roma.

'Yan wasa Erick Pulgar da kuma Franck Ribery suka ci wa Fiorentina kwallaye, ita kuwa Milan, Brahim Diaz da kuma Hakan Calhanoglu ne suka yi mata bajintar, bayan da Ibrahimovic ya ci na farko.

Milan ta koma ta biyu a teburin Serie A da maki 59 da tazarar maki shida tsakaninta da Inter ta daya kawo yanzu.

Sai dai kuma Inter tana da kwantan wasa daya, bayan da aka dage wasan da ya kamata ta buga da Sassuola, bayan samun wasu yan kwallo dauke da cutar korona.

Fiorentina ta ci gaba da zama ta 14 a kasan teburi mai maki 29 da tazarar maki bakwai tsakaninta da 'yan ukun karshen a gasar ta Serie A.

Source: BBC