Menu

Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga taka leda

Zlatan Ibrahimovic

Mon, 5 Jun 2023 Source: BBC

Dan kwallon AC Milan, Zlatan Ibrahimovic ya yi ritaya daga taka leda yana da shekara 41 da haihuwa.

Tun a baya Ibrahimovic ya sanar cewar zai bar Milan mai buga Serie A.

Ya ci kwallo 511 a ƙungiyoyin Paris St-Germain da Manchester United da AC Milan da Inter Milan, tare da lashe kofi a gasar kasashen Turan huɗu.

Ibrahimovic ya koma taka leda a AC Milan a 2020, inda ya lashe Serie A a 2021.

Dan wasan ya fara wasa a matakin ƙwararren ɗan kwallo a Malmo FF a 1999 daga nan ya koma Ajax a 2001, wadda ya yi kaka uku tare da ɗaukar kofin ƙasar uku.

Ya koma Juventus a 2004, ƙungiyar da ya lashe kofi biyu daga baya aka karɓe su a wani hukuncin da aka samu ƙungiyar da cogen wasannin.

Dan ƙasar Sweden ya ƙara ɗaukar kofi uku a Serie A daga nan ya koma Inter Milan, bayan nan ya je Barcelona a 2009.

Kaka ɗaya Ibrahimovic ya yi a ƙungiyar Camp Nou da ɗaukar La Liga, sai aka bayar da aronsa ga AC Milan daga nan kungiyar ta Italiya ta mallaki ɗan kwallon a 2011.

Ibrahimovic ya koma Paris St-Germain, ƙungiyar da ya ci wa ƙwallo 113 a wasa 122 a lik da lashe kofin Ligue 1 huɗu.

A watan Yulin 2016 ya saka hannu a Manchester United kan kaka biyu a ƙungiyar da ke buga Premier League, wanda ya ɗauki League Cup da kuma Europa League.

Dan wasan gaban ya koma buga gasar Amurka ta MLS a ƙungiyar LA Galaxy a 2018, inda ya yi kaka biyu a California daga nan ya sake komawa AC Milan.

Source: BBC