BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ɗaliban Nijar a Sudan sun nemi ɗaukin hukumomi

Hoton alama

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

Ƴan Nijar da ke zaune a Sudan musamman dalibai, na kokawa kan yadda har yanzu ba wani yunkuri da gwamnatin kasar ke yi don kwashe su zuwa gida,.

Suna wannan koke ne a daidai lokacin da kasashen duniya daban-daban ke ci gaba da kwaso mutanensu da ke zaune a Sudan bayan da yakin da ke faruwa tsakanin sojojin gwamnati da na rundunar mayakan RSF a kasar ya rutsa da su.

Daliban Jamhuriyar Nijar din da da ke karatu a kasar ta Sudan sun ce suna cikin wani hali na tsaka mai wuya bayan da wakilan karamin ofishin jakadancin ƙasar da suke sa ran samun taimako daga gare su suka bi tawagar kasar Faransa zuwa Djibuti suka bar su a zube.

Alhaji Rabi’u Kane ɗaya ne daga cikin jagororin daliban kasar ta Nijar da ke Sudan inda ya ce yanzu suna cikin tsakiyar inda tashin hankalin yake.

‘’Ta ko ina an saka mu tsakiya, karshe ma har harbe-harbe ake yi a tsakiyar inda dalibai suke, don yanzu haka babu dalibi ko daya a cikin dakunan kwana, mun tattare kaya muna kwana a tsakiyar fili na jami’a saboda gudun kada wani gini da rugozo wa mutum,’’ in ji shi.

Ya kuma ce a halin da ake ciki yanzu ba su san inda za su sa kansu ba, saboda dama inda ya kamata su kai kukansu ofishin huldar jakadanci ne "kuma mun je".

Ya kara da cewa: ‘’Mun je mun kai kanmu, kuma su kan su wadanda ya kamata su jagorance mu sun bi tawaga ta kasar Faransa sun tafi sun bar mu.’’

Daliban sun kuma yi kira ga shugaban Nijar Mohammed Bazoum da ya taimaka musu ya dauki matakin da ya dace don fitar da su daga cikin wannan tashin hankali da suka fada ciki.

‘’Ba mu da kowa sai Allah sai kai shugaban kasa, kai ne za ka iya taimakawa ka fitar da mu daga cikin wannan tashin hankali saboda halin yaki ba a san inda zai kai mu ba, mun shiga wani yanayi wanda babu wanda zai iya taimaka mana sai kai, saboda kai ne babanmu, a cewar dalibi Rabi’u.

‘’Sauran kasashe kowa ya zo suna kula da mutanensu suna kwashe su.’’

Ita ma dai kungiyar dalibai ta kasa USN ta bakin kakakinta Ifredi Maulil Alasan ta yi kira ga hukumomin kasar da su yi kokari su kwaso daukacin daliban na Jamhuriyar Nijar zuwa gida.

‘’Yadda sauran kasashe suka mayar da dukkan ‘yan kasarsu gida, mu ma hukumomin kasarmu ya kamata su gaggauta tura jirage don kwaso duk wani dan kasar zuwa gida,’’ in ji shugaban kungiyar.

Shi ma shugaban kungiyar da ke fafutikar kare hakkin dan adam ta MUJEN Surajo Isa ya koka da wannan matsala yana mai cewa sun nemi jin ta bakin ofishin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar din game da wannan batu.

Ya ce a matsayinsu na kungiyoyin fararen hula tun da aka fara wannan yaki a Sudan suka tuntubi ofishin ministan harkokin waje a ƙasar, inda suka bayyana mana cewa shugaban kasa ya bayar da umarni na a dauki matakan ganin cewa an maido da duka ‘yan kasar Nijar da wannan yakin ya rutsa da su zuwa gida, kuma mun yarda da cewa shugaban kasa Bazoum Mohammed yana biye da wannan magana sannan kuma za a dauki matakai.

Ofishin ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar din ya ce nan gaba kadan ne zai fitar da wata sanarwa game da wannan batu, sai dai a nata bangaren ma’aikatar kula da harkokin Turai da ma ma’aikatar harkokin sojin kasar Faransa sun gudanar da aikin kwashe mutane daga birnin Khartoum.

Da safiyar yau ne Talata ne aka kwashe mutane 538 zuwa kasar Djibouti, daga ciki ‘yan kasar Nijar 38 maza da mata da kananan yara.

Source: BBC