BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ɗalibin da ya tsallaka ƙasa biyar don zuwa aikin Hajji a ƙafa

Usman Arshad a yanzu yana cikin miliyoyin mahajjata

Mon, 26 Jun 2023 Source: BBC

Yayin da maniyyata sama da miliyan ɗaya da 300,000 da suka je Saudiyya daga sassa daban-daban na duniya suka fara gudanar da ibadar Aikin Hajji a bana, maimakon hanyar da aka saba bi, wani ɗalibi daga Pakistan ya je hajjin ne a ƙafa.

Ya shafe tsawon wata shida yana tattaki kafin ya isa ƙasar Saudiyya daga bisani.

Usman Arshad a yanzu yana cikin miliyoyin mahajjatan da ke gudanar da wannan ibada wadda duk Musulmi yake fatan zuwa idan ya samu iko.

Source: BBC