Menu

Ɗan sanda a Ghana ya manta da bindigarsa wajen karɓar cin hanci

Di rifle wey oga police leave for inside moto

Mon, 30 Jan 2023 Source: BBC

Wani ɗan sanda a ƙasar Ghana ya shiga tsaka-mai-wuya bayan da ya mance da bindigarsa a cikin wata motar haya.

Direban motar ya yi zargin cewa ɗan sandan ya bar bindigarsa ne bayan da ya karɓi cin hanci.

A wani bidiyo da ake yadawa a shafukan soshiyal midiya, an ga wani direba yana rike da bindiga kirar AK-47.

Direban motar hayan ya mayar wa 'yan sanda bindigar inda ya bayyana musu cewa dan sanda ne ya mance da ita a cikin motarsa a lokacin da ya shiga domin kabar cin hanci.

Hukumomi sun kama ɗan sandan

A sanarwar da ƴan sanda suka fitar, sun sanar da kama Sufeto Sulemana Adam wanda ke aiki tare da runduna ta musamman a Takoradi da ke yammacin kasar.

Kakakin rundunar Olivia Adiku ya ce "Hukumar 'yan sanda ta kama wani sufeto wanda ya yi ganganci a aiki ta hanyar barin bindigarsa a cikin wata motar haya".

A yanzu haka an gabatar da batun gaban sashen kula da ɗa'a na 'yan sanda kuma dan sandan da direban motar duk suna bayar da hadin kai wajen binciken da ake gudanarwa.

Source: BBC