BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ƴan sandan Najeriya sun koka kan rashin biyansu kuɗin alawus

73446213 Hoton alama

Mon, 1 Jan 2024 Source: BBC

Ƴan sandan kwantar da tarzoma da aka tura yankin arewa maso gabashin Najeriya, sun koka kan rashin biyan su kuɗaɗen alawus na tsawon watanni shida.

’Yan sandan, wadanda aka ɗebo daga jihohi daban-daban aka kai su yankin don gudanar da ayyukan samar da tsaro tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun ce rashin biyan su kuɗaɗen ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Wani daga cikin ƴan sandan da abin ya shafa ya shaida wa BBC cewa tun da aka tura su yankin wata takwas da suka gabata domin aiki tare da sojoji, alawus ɗin wata biyu kacal aka biya su, duk kuwa da cewa suna ganin takwarorinsu na samun nasu alwaus ɗin a kan kari.

'Muna fuskantar matsaloli sakamakon rashin samun kuɗaɗen na alawus, saboda albashinmu ne kaɗai muke rabawa da iyalanmu kuma muna kula da hidimomin kanmu. A cikin wannan albashin ne muke kula da matsalolin lafiyarmu, mu kuma ci abinci da magance sauran abubuwan da suka rataya a wuyanmu a matsayinmu na masu iyali.'

Ya kuma yi kira ga shugabanninsu da su saurari roƙon da suke yi a biya su hakkokinsu ganin cewa akasarinsu daga wurare masu nisa aka kai su kuma a halin yanzu suna cikin mawuyacin hali.

Yunƙurin da BBC ta yi na ji daga bakin hedikwatar rundunar 'yan sandan Najeriya game da wannan batun ya ci tura sakamkon rashin amsa kiraye-kirayen wayar da aka yi zuwa sashen hulɗa da jama'a na rundunar.

Yayin da waɗannan ƴan sandan ke sadaukar da rayukansu ga ƙoƙarin kwantar da tarzomar tsaro a yankin arewa maso gabashin ƙasar, akwai buƙatar a ga cewa ana biyansu haƙƙoƙinsu a kan lokaci domin su sami damar gudanar da ayyukansu ba tare da wata tangarɗa ba kamar yadda masu sharhi ke gani

Source: BBC