Ƴan sanda a Sifaniya sun kama wasu mutane uku masu goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Valencia bisa zarginsu da cin zarafin dan kwallon kungiyar Real Madnid Vinicius Junior ta hanyar kalaman wariyar launin fata.
Daga cikin mutanen uku har da wani bakar fata, sanna kuma ƴan sandan sun sanar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da rataye mutum-mutumin Vinicius din.
Lamarin ya janyo ka-ce-na-ce a Brazil, sannan gwamnatin kasar ta bukaci ganawa ta musamman da ministocin Sifaniya da masu gabatar da kara da kuma hukumar kwallon kafar kasar.
A lokacin karawar Valencia da Real Madrid ne aka ci zarafin Vinicius, wanda karon farko kenan da aka ba shi jan kati a tarihin sana'arsa ta ƙwallo.
Ɗan wasan mai shekara 23 ya fuskanci kalaman wariya da na cin zarafi karo da dama a La Liga a kakar nan.
An dan dakatar da karawar a zagaye na biyu, bayan da dan kwallon Real din ya nuna bacin ransa kan kalaman wariyar da magoya bayan Valencia suka dinga furtawa a filin wasan.
Daga lokacin ne ransa ya baci har ta kai da aka ba shi jan kati a fafatawar da aka ci Real 1-0, karo na takwas da ta yi rashin nasara a La Liga a bana.
Ita kuwa Valencia, wadda ta ci wasan ta yi sama zuwa ta 13 da tazarar maki biyar tsakaninta da 'yan ukun karshen teburin La Liga.