BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ɗan ƙwallo mafi tsufa a duniya ya tsawaita zamansa a Portugal

Kazuyoshi Miura

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

Kazuyoshi Miura, dan wasan kwallon kafa mafi tsufa a duniya mai shekaru 56, ya tsawaita zamansa da kungiyar Oliveirense ta Portugal da ke wasa a mataki na biyu.

Tsohon dan wasan na Japan ya koma Oliveirense a matsayin aro a watan Janairu daga Yokohama kuma zai ci gaba da zama tare da su na tsawon lokaci da ba a bayyana ba.

Miura ya buga wasan kwallon kafa na mintuna 28 kacal a bana, inda ya buga wasanni uku bayan da ya maye gurbin wasu.

Gungun mutane ɗaya ne suka mallaki Yokohama da Oliveirense.

Miura, wanda ya fara taka leda da kungiyar Santos ta Brazil a shekarar 1986, ya kasance a Yokohama FC tun 2005 - ko da yake ya yi zaman aro a 2022 a Suzuka Point Getters na mataki na hudu, wanda babban yayansa Yasutoshi ke kula da shi, inda ya ci kwallaye biyu a wasa18.

Ya kuma buga kwallo a Italiya da Croatia da kuma Australia.

Shahararren dan wasan kwallon kafa na ƙasar Japan ya zura kwallaye 55 a wasanni 89.

A baya ya ce zai ci gaba da wasa har sai ya kai shekaru 60.

Source: BBC