Menu

Ƙarairayin da ke rura wutar ƙyamar ƴan ci-rani a Tunisia

Hoton wasu yan Ivory Coast da suka dawo gida daga Tunisia

Fri, 10 Mar 2023 Source: BBC

Ana ta yaɗa hotunan bidiyo na bogi game da ƴan ci-rani daga yankin ƙasashen Afirka na baƙar fata Tunisia a dai-dai lokacin da ake ta bayyana ra'ayoyi game da yaƙi da baƙin haure a ƙasar.

Shugaba Kais Saied na Tunisia ya ce yin hijira wani shiri ne na sauya fasalin ƙasar sannan Ivory Coast da Guinea sun soma kwashe jama'arsu saboda kare su daga matsala.

Mun duba bidiyo da dama da suka karaɗe shafukan intanet da ke iƙirarin nuna baƙin haure a Tunisia, kusan dukkansu an yi su ne a wasu wuraren daban ba ainahin inda ake cewa can ne ba.

Ba a Tunisia baƙin haure suka yi zanga-zanga ba

Bidiyon Tiktok da dama da aka wallafa a baya-bayan nan sun nuna gomman 'yan ƙungiyoyi suna gudu a kan titi a abin da ake ganin zanga-zangar nuna adawa ce.

Ɗaya daga cikin hotunan bidiyon da miliyoyin mutane suka kalla an yi masa take da Larabci da ke nufin "Mamaye Tunisia"

Wani bidiyon kuma ya bayyana cewa "Tunisia ta zama matattarar ƴan Afirka."

To amma kuma wannan dandazon da aka nuna a bidiyon ya faru ne a Dakar, babban birnin Senegal.

Ta bayyana ƙarara cewa an ɗauki bidiyon ne daga wani ginin tarihi, wanda ake iya ganinsa yayin da mai naɗar bidiyon ke kai-komo.

Wuri ne da ke Place de l'Obélisque a Dakar wanda ake iya gani a taswirar Google.

Ana kuma iya ganin tutar Senegal sannan mun tabbatar cewa yaren da suke yi a bidiyon shi ne Wolof, harshen ƙasar Senegal.

Mun kuma gano cewa taro ne da ƴan hamayya suka yi a Dakar cikin watan Yunin 2022, ana kuma iya kallon bidiyon idan aka taɓa nan.

Ba ƴan ci-rani ne suka haifar da cunkoson ababen hawa ba

Akwai wasu hotunan bidiyo da aka wallafa a Tiktok da suke iƙirarin cewa zang-zangar da ƴan ci-ranin Afirka suka yi, a Tunisia aka yi.

Babban misali shi ne gungun mutane da ake ganin sun fito ne daga yankin kudu da hamadar sahara suna fito na fito da direbobi da wadanda ke tsaye a gefen titi yayin da motoci ke tsaye cik ba sa tafiya.

An yi wa bidiyon take da Larabci: "Mamayar da ƴan ci-ranin Afirka suka yi wa Lardunan Tunisia."

Wasu da a cikin ra'ayoyin da aka yi a kan bidiyon sun nuna cewa ba Tunisia ba ne, Morocco ne kuma mun tabbatar da haka daga alamomin da muka gani daga bidiyon.

Wata jar mota a bidiyon tana da alamar da aka yi a samanta da ke cewa "ƙarami" a Larabci wanda wata alama ce ta motocin tasi masu launin ja a birnin Casablanca na Morocco.

Duk da cewa ba a iya tantance lambar motar ta baya ba, lambobin ba su kai biyar ba, kamar yadda yake a lambobin motoci a Morocco.

Mun kuma duba irin tattaunawar da ake a bidiyon kuma irin Larabcin da suke ya yi dai-dai da wanda ake yi a Morocco.

Waɗan nan ƴan ci-rani ba Tunisia suka nufa ba

Wani bidiyo da aka wallafa a baya-bayan nan a shafin Tiktok ya nuna wasu gungun maza suna tafiya a hamada inda aka rubuta a "Gungun ƴan Afirka baƙaƙen fata suna tsallaka hamada zuwa Tunisia."

Sai dai mun ga wani shafin TikTok da ya nuna bidiyon amma ya fi tsawo.

Wani mutum ne da ke ɗaukar bidiyon ficewarsa daga Algeria ya wallafa shi a Satumban 2022 bayan da aka tilasta masa ya fice.

Bidiyon na biyu ya fi fitowa kuma a jiki akwai rubutu da ya rufe wani ɓangare na hotunan.

Amma duk da haka wasu sun bayyana cikin gungun da suka saka kaya iri ɗaya har da wani mutum da ya ɗora jaka mai ratsin ruwan hoda da fari a kansa.

An kori dubban baƙin hauren kudu da hamadar Sahara daga Algeria a shekarar da ta gabata, a cewar ƙungiyoyin agaji.

A wani bidiyon da mutumin ya wallafa, ya ce ya isa Bamako, babban birnin Mali wanda zai haɗa tafiya mai wahala a hamadar sahara.

Babu gaskiya baƙin haure sun isa a motoci masu sulke

Wani bidiyo da dubban mutane suka kalla ya nuna motoci cike da masu riƙe da makamai na tafiya kan titi sannan ga masu kallo a gefen titin.

An rubuta "Suma ƴan Afirka na da makamai."

Sai dai mun gano wasu da suka wallafa irin bidiyon inda suka ce an naɗe shi a Sudan kuma akwai wasu bayanai a bidiyon da suka tabbatar da haka.

Akwai wani shago a kan titi da aka yi wa alamar "Tappc", wani kamfanin sayar da mai da ke da mazauni a Sudan.

Mun kuma ga wani tambari mai launin fari da ja da kore a jikin ɗaya daga cikin motocin da ke wucewa wanda launuka ne na tutar Sudan.

Mun yi ƙoƙarin haɗa bayanan da alamar da ke jikin kayan sarkin da sojojin na Sudan suka sanya.

Jar hula da farar ɗamara ɗin da sojojin suka sa, an san wasu rundunonin na sojojin Sudan suna sanya su.

Sannan wata alama ta ƙarshe - ɗaya daga cikin shagunan da ke bidiyon an rubuta "rakshat" da Larabci, wato yadda ake kiran baburan haya masu ƙafa uku-uku a Sudan.

Tsohon bidiyon abin da ya faru a tashar jirgi

A wasu lokutan, ana amfani da hotunan bidiyo domin neman a tausaya wa ƴan ci-rani baƙaken fata a Tunisia.

Misali shi ne saƙon da aka wallafa a Tuwita na wani abu da ya faru a filin jirgin sama na Tunisia inda aka nuna wani mutum ana sa-in-sa da shi kuma ma'aikatan filin jirgin da jami'an tsaro suka kuma dakatar da shi.

"Ƴan Afirka baƙar fata na fuskantar cin zarafi a Tunisia ko da a lokacin da suke ƙoƙarin ficewa.....", kamar yadda saƙon ya bayyana.

Wannan abu dai ba a Tunisia ya faru ba amma a ra'ayoyin da aka rubuta a ƙarƙashi sun nuna cewa an yi ne tun Yulin 2022.

Kafafen yaɗa labarai da dama, ciki har da a Birtaniya, sun bayar da rahoton a lokacin. Ba wai na yanzu ba ne.

Amma duk da haka ba shakka akwai bayanan cin zarafi da muzgunawa da ake nunawa baƙin haure baƙaƙen fata a Tunisia, lamarin da ke jefa mutane da dama cikin fargabar rashin tsaro.

Nazari da rahoto daga Abdirahim Saeed da Alioune Diop da Alphonse Dioh da Taouba Khelifi da Kumar Malhotra da Peter Mwai da kuma Raissa Okoi

Source: BBC