BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ƙarin bazuwar ƙwayar a-rungumi-zaki a Najeriya na tayar da hankula

Hoton alama

Thu, 13 Jul 2023 Source: BBC

Hukumomi a Najeriya na bayyana damuwa a kan yadda wata muguwar ƙwaya da ake kira a-rungumi-zaki (metamphitamine ko meth) ke daɗa bazuwa a wasu sassa na arewacin ƙasar saboda girman hatsarinta.

"Yanzu gaskiya a nan Sokoto ta addabe mu. Du yawancin kamen da muke, sai ka ga mun kama wannan ƙwaya," in ji kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta jihar Sokoto.

Adamu Iro Mohammed ya ce ƙwayar ta fi hodar iblis hatsari, saboda masu shan ta suna iya aikata komai idan suka bugu.

A cewarsa, ƙwayar a-rungumi-zaki ko meth ita ce ta fi tayar da musu da hankali a baya-bayan nan cikin jihar Sokoto, "duk aikin da muke yi".

Ya ce ƙwaya ce mai saurin shiga rai, kuma da zarar mutum ya fara sha, to zai yi ta faman neman yadda zai yi ya same ta, don ya sha, ya ji daɗi a ransa.

Jami'in ya bayyana haka ne ranar Alhamis lokacin da yake zantawa da BBC bayan ƙona wasu nau'o'in kayen mayen da hukumar ta kama a tsawon shekara goma sha shida.

"Yanzu haka ma, muna da mutane waɗanda muka kama sun kai biyar dukkansu masu dillancin wannan ƙwaya," cewar Adamu Iro Muhammed.

Shi ma, kwamandan NDLEA na jihar Kano, Sadiq Idris Abubakar ya ce su ma suna ganin ƙaruwar ƙwayar a yanzu.

Ya ce ana kiran ƙwayar da sunan a-rungumi-zaki ne saboda yadda take birkita tunanin mutum gaba ɗaya, ta yadda tausayi da tsoro za su gushe daga zuciyar mutum.

"Dukkan abu na hatsari, masu shan ƙwayar na iya rungumarsa ko ya faɗa masa," in ji Sadiq Abubakar.

Ya ce tsadar wannan ƙwaya ta a-rungumi-zaki ta sa a baya tana da wahalar samu a cikin gida, saboda akasari masu sarrafa ta suna yi ne, sannan su fita da ita zuwa ƙasashen waje.

A cewar Adamu Iro Mohammed, ƙwayar a-rungumi-zaki ta fara maye gurbin sauran miyagun ƙwayoyin da suka sani a yankin Sokoto. Ya ce ita ce suka fi gani matasa na daɗa runguma a madadin tabar wiwi da magungunan tari masu sinadarin kodin.

"Kuma abin nan gaskiya bisabi lillahi matsala ne ba kaɗan ba!"

Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyin sun ce akasari ana yin ƙwayar ne a ɗakunan sirri na sarrafa kayan maye.

Shi dai kwamandan NDLEA na jihar Sokoto ya ce bincikensu ya gano cewa masu sarrafa maganin mayen da ake kira A-kuskura suna haɗawa ne da ƙwayar A-rungumi-zaki.

Shi ya sa kake gani idan mutum ya sha, duk ya rikice ba ya cikin hayyacinsa, in ji shi

Source: BBC