Menu

Ƙarin kuɗin makarantu ya jefa iyaye tasku a Najeriya

School Children Nigeria 1234 Hoton alama

Thu, 14 Sep 2023 Source: BBC

Iyayen da maruƙan yara a Najeriya sun shiga wani yanayi na tasku da ƙaƙa-ni-kayi sakamakon ƙarin kuɗin makaranta da galibin makarantu masu zaman kansu suka yi a faɗin ƙasar.

Iyayen na wannan koke ne yayin da aka buɗe makarantun boko a duk fadin ƙasar bayan dogon hutu, domin fara sabuwar shekarar karatu.

Yawancin iyaye da mariƙan na cewa wannan yanayi ya jefa su cikin hali na tababa game da cigaban karatun 'ya'yan nasu ganin cewa kuɗaɗen da suke samu ba su ƙaru ba yayin da ɗawainiya ta tsadar rayuwa ta ƙaru sosai.

Ƙarin kuɗin ya zo ne a wani lokaci da aka sami koma-baya game da kuɗin da iyalai ke samu, musamman saboda fadi tashin hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka, wanda cire tallafin man fetur ya haddasa.

Shauƙi da damuwa

A irin wannan lokaci na komawa makaranta yawancin yara na kasancewa cikin murna da shauƙi na komawa makaranta.

Sai dai kuma komawar a wannan karon ta zo wa iyaye da damuwa, sakamakon ƙarin kuɗin makarantun da yawancin makarantu masu zaman-kansu suka yi a duk faɗin ƙasar.

Matsin tattalin arziki da tsauwalar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar ne suka tilasta ƙarin kuɗin na makaranta, a cewar jami'ar wata makarantar kuɗi da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyar:

''Kowa dai ya san matsalar ya zama ruwan dare ya shafi kowa da kowa shi ya sa muka yi ƙarin kuɗin makaranta.''

Jami'ar ta ƙara bayani da cewa, '' ka ga za a biya malamai ga haraje-haraje da ake biya ga kuɗin sayen takardu, abin rubutu ga su nan dai kuɗin wuta kuɗin ruwa da sauransu.''

Ta ce, su ma ba da sonsu suke ƙara kuɗin ba domin idan ba su yi hakan ba ta yaya za su iya biyan malamai, har a samu yaran su yi karatu?

Fatan gyara

Wannan karin kuɗin makaranta dai ya jefa iyaye cikin halin kaka-ni-ka-yi, kamar yadda wani magidanci mai ƴaƴa biyu ya bayyana wa BBC.

Ya ce a wancan zangon karatun ƴarsa ɗaya tana makarantar renon ƙananan yara ɗaya kuma tana furamare.

Bayan da aka yi ƙarin kuɗin a yanzu ɗaya an ƙara naira dubu ashirin da biyu a kan kuɗin da ya biya wancan lokacin ɗaya kuwa an ƙara naira dubu ashirin da ɗaya.

''Ga shi kuma ba a yi ƙarin albashi ba kuma an ƙara maka kuɗin makaranta,'' yana kokawa da halin.

Ya ce a tattaunawar da suka yi da wasu takwarorinsa iyayen yara, ya ce wasu ma na tunanin cire yaran su mayar da su wasu makarantun masu ɗan sauƙin kuɗi.

''Fatanmu gaskiya gwamnati ta gyara, domin da ta gyara makarantunta tana biyan malamai albashi yadda ya kamata da iaye da dama ba za su kai ƴaƴansu makarantu masu zaman kansu ba,'' in ji shi.

Al'amarin dai ya fara shafar yadda ake tafiyar da hidimomin gida, a cewar wata matar aure: ''Mu da muke da yara uku huɗu biyar gaskiya abin yana mana wahala sosai, sannan kuma yanzu makarantu sai su ce sai ka biya ɗanka zai fara zuwa makaranta.''

''Ga kuɗin litattafai ga kuɗin yunifom ga kuɗin sauran abubuwa da ciyarwa abin ya taɓa iyaye gaskiya ta kowa ne ɓangare, saboda yanayin abin da kake samu,'' a cewarta.

A yanzu dai iyaye da dama sun zura ido ne, su ga irin yadda sassauci zai samu daga alƙawuran tallafi ta hanyoyi daban-daban da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi wa al'ummar ƙasar, bayan cire tallafin man fetur.

Source: BBC