BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 6 a Anambra

 117628673 4e1d2976 8819 4517 8a9e 91a80bc6410d Jami'an tsaro akalla shida ne suka hallaka a jihar Anambra

Fri, 19 Mar 2021 Source: BBC

Jami'an tsaro akalla shida ne suka hallaka a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Jami'an tsaron sun hada da sojojin ruwa uku da wasu yan bindiga suka harbe a garin Awkuzu da ke karamar hukumar Oyi.

Sai kuma jami'an 'yan sanda uku da yan bindigar suka harbe a Neni da ke karamar hukumar Anaocha tare kuma da cinna wa motarsu wuta.

Al'amarin ya janyo zaman zulumi a jihar kuma ana rade radin cewa an sami wani gungun 'yan bindiga da ke kai wa jami'an tsaro hari a jihar ta Anambra.

Rahotanni sun ce yan bindigar sun harbe sojin ruwan ne da karfe biyu na rana inda suka yi awon gaba da makamansu.

Jihar Anambra na cikin jihohin da aka hallaka jamian 'yan sanda tare da kona caji ofis na yan sanda a watan Fabarerun daya gabata.

Source: BBC