Virginia ta zama jiha ta farko a Kudancin Amurka da ta soke hukuncin kisa bayan da gwamnan jihar ya sa hannu a kan dokar da ta kawo karshen hukuncin.
Gwamna Ralph Northam ya ce sokewar za ta kawo karshen tsarin kashe mutane. Tarihi ya nuna cewa akwai wariyar launin fata.
Matakin na zuwa ne dai dai lokacin da aka sabunta muhawara a kasa baki daya a kan batun da ya shafi hukuncin kisa.
Virginia ta aiwatar da hukuncin kisa kan mutane da dama kuma ta fi sauran jihohi aiwatar da hukuncin kisa in banda jihar Texas tun bayan da kotun koli ta daukaka hukuncin kisa a shekarar 1976.
Tun bayan wannan lokaci akasarin hukuncin kisa na faruwa ne a jihohn da ke Kudancin Amurka wadanda a baya sun kasance jihohi da suka amince da cinikin bayi.
Sai dai akwai wasu jihohi 27 da ba su amince da hukuncin kisa ba ko da yake akwai wasu jihohi da suka kafa dokar da ta soke aiwatar da hukuncin kisa.
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake dawo da hukuncin kisa a matakin tarayya a bara bayan shekara 17 da soke dokar.
An yanke wa murum 13 hukuncin kisa a cikin yan watanni ciki har da mutum 6 da aka aiwatar wa hukuncin kisa bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasa.
A lokacin yakin neman zabensa , Joe Biden ya sha alwashin kawo karshen hukuncin kisa a matakin tarayya kuma ya nemi jihohi su bi sahun gwamnatin tarayya.