Kwamitin tsaro da tabbbatar da zaman lafiya na kungiyar kasashen Afirka, AU, zai yi wani taro a yau Alhamis domin tattauna dambarwar siyasar da ake ciki a kashashen Chadi da Somalia.
A wata 'yar takaitacciyar sanarwa da kakakin kungiyar ta AU chairperson Ebba Kalondo ya fitar ya ce taron na daga tanadin aikin kwamitin a matsayinsa na yanke hukunci kan karewa ko sasanta wani rikici a nahiyar Afirka.
kwamitin tsaro na kungiyar ta kasashen Afirka ya bayyana wannan mataki ne kwana daya bayan da 'yan hamayya na kasar Chadi suka sanar da kin amincewarsu da nadin rundunar sojin kasa ta Chadi ta yi wa dan marigayi Shugaba Idriss Déby na karbar mulki bayan mutuwar mahaifin nasa.
Marigayin mai shekara 68 - wanda ya kasance a kan mulki tsawon shekara talatin, ya rasu ne bayan da aka harbe shi a fafatawa da 'yan tawaye a fagen daga. Ana daukar Chad a matsayin mai matukar muhimmanci a kan batun yaki da masu ikirarin jihadi a Afirka.
Ita ma Somalia wadda taron na kwamitin tsaron na kungiyar ta AU, zai tatauna batunta, tana fama da rikici ne na tsarin mulki sakamakon dambarwar da ta bzaben shugaban kasa da na 'yan majalisa.
A makon da ya gabata ne shugaban kasar ta Somalia Mohamed Abdullahi "Farmajo" Mr Farmajo, ya amince da tsawon wa'adinsa a kan mulki da shekara biyu, kamar yadda majalisar dokokin kasar ta amince.
Abin da hukumomi da manyan kasashen dunbiya da suka hada da Amurka da Birtaniya da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar Tarayyar Turai da kungiyar kasashen Afirka, AU suka yi Allah-wadai da shi, inda suka nemi da a samar da matsaya wajen sasanta dambarwar, da suka ce ta kara tsunduma kasar cikin rikicin siyasa, da ka iya rikita yanking aba daya.
Shi dai kwamitin tsaron da tabbatar da zaman lafiya na kungiyar ta kasashen Afirka zai iya bayar da shawarar sanya takunkumi a kan wata kasa wadda ta saba dokokin kungiyar a kan dumokuradiyya da shugabanci, matakin da ya hada da dakatar da kasa daga cikin kungiyar.