BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Me ya sa‘yan siyasa suka daina hada hotunansu da na Muhammadu Buhari a fosta?

48846483 Shugaba Muhammadu Buahri

Wed, 7 Dec 2022 Source: BBC

Yayin da ake ci gaba da yakin neman zabe don babban zaben Najeriya na shekarar 2023, wani abu da aka lura da shi, shi ne yadda ‘yan takara suka daina amfani da hoton shugaba Muhammadu Buhari a fastocinsu.

A baya 'yan siyasa musamman a lokutan zaben 2015 da na 2019, sun yi ta rububin hada hoto da Buhari, wajen tallata kansu da "Mai Gaskiya" kamar yadda suke yi masa kirari, kuma ana ganin da dama sun dare madafun iko ne, da rigar shugaban.

A yanzu duk inda aka zaga a ko ina a jihohin Najeriya, sai da aga hotunan ‘yan takara da wasu ‘yan siyasar musamman shugabannin jam’iyya da makamantansu.

‘Yan siyasar da suka yi amanna da akidu da manufofin shugaba Muhammadu Buhari, musamman a jihar Kano da ke arewa maso yamacin Najeriya, a yanzu sun daina amfani da hotunan shugaban a yayin neman goyon bayan masu kada kuri’a.

Duk da kasancewar jihar ita ce inda aka fi nunawa shugaban tsantsar soyayya, ayanzu komai ya canja domin duk inda ka zaga a jihar sai dai kaga hotunan ‘yan takarar tare da na shugaban APC dana gwamnan jihar ko kuma wani jigo a jam’iyyar.

Wasu mazauna birnin na Kano da BBC ta zanta da su sun ce mutane sun riga sun gaji da mulkin shugaban ne shi yasa ko damuwa basa yi don dan takara bai hada hotonsa dashi ba a fosta.

To amma duk da haka wasu mazauna Kanon sun ce har gobe su suna son shugaban kuma ba zasu taba daina sonsa ba, hasalima koda za a ce zasu tsaya takara to  zasu hada hotonsu da na Buharin a fosta.

To ko masu sharhi kan al’muran siyasa a Kanon ke kallon lamari?

Farfesa Kamilu Sani Fagge, malami ne jami’ar Bayero dake Kano, ya shaida wa BBC cewa, wannan al’amari nada nasaba da rashin tasirin ‘Sak’ da aka yi a baya domin a yanzu hakan ya ragu.

Ya ce,” A da mutane sun shiga rigar shugaba Muhammadu Buhari, inda aka zabe su ba tare tabbatar da cancanta ko rashin cancantarsu ba, amma a yanzu farin jinin shugaba Buharin ma ya ragu, don haka ‘yan takara sun san hada hotonsu da shi ma ba wani abu da zai kara musu.”

Duk da kasancewar mutane da dama a Najeriyar sun dawo daga rakiyar gwamnatin shugaban, har yanzu akwai wadanda ‘yan gani kashenin shugaban ne duk sukar da ake masa.

An yi wani zamani da ya shude, wanda a cikinsa kowanne dan takar tun daga ta Kansila har zuwa 'yan majalisu da na gwamnoni kan cika hotunan shugaba Buhari a jikin fasta ko allon tallata hajar sa.

Kuma, mutane da dama a sun yi amanna duk wanda ke tare da shugaba Muhammadu Buhari to kuwa mai gaskiya da rikon amana ne.

Source: BBC