BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Manyan kalubale 5 da Tinubu zai fuskanta a matsayin sabon shugaban Najeriya

Sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu

Tue, 30 May 2023 Source: BBC

Ana yawan bayyana Najeriya a matsayin uwa ma ba da mama a Afirka saboda yawan al'ummarta da kuma karfin tattalin arzikinta sai dai tana fama da wasu gagaruman matsaloli - da za su tunkari Bola Tinubu yayin da yake shirin karbar mulki ranar Litinin.

Ba lalle bane Tinubu mai shekara 71 ya damu da kalubalen. A matsayinsa na wanda ya jagoranci jihar Legas a matsayin gwamna sau biyu, ya farfado da cibiyar kasuwancin ta Najeriya - wani lamari marar sauki kuma ya san da batutuwan.

Sai dai 'yan Najeriya, da wadanda ma ba su jefa masa kuri'a ba, za su so su ga sauyi cikin hanzari daga Tinubu. Ga wasu daga cikin manyan kalubalen da zai fuskanta da ma yadda watakila zai warware su.

Soke tallafin man fetur

Wannan kalubale ne da gwamnatocin baya suka yi saurin sauyawa tun bayan da aka kaddamar da shi a shekarun 1970.

Duk da kasancewar Najeriya na da arzikin man fetur, kasar ta kasa tace danyen manta domin biyan bukatun kasa a don haka take shigo da albarkatun man fetur wadanda kuma ake sayarwa kan farashin da gwamnati ta kayyade. Kasancewar akasari farashin yana kasa da farashin da ake shigo da shi, sai gwamnati ta rika biyan tallafin.

Amma tallafin yana shafar harkokin kudi na gwamnati. A shekarar da ta gabata, gwamnatin ta kashe naira triliyan 4.3 kwatankwacin dala 9.3 kan tallafin mai sannan cikin wata shida na wannan shekara, an ware naira triliyan 3.36 domin wannan bangare.

Kudaden da ake biya na shafar ayyukan gina al'umma kamar makarantu da asibitoci amma cire tallafin ba zai zo da sauki ba saboda zai janyo hauhawar farashin kayayyaki.

Yunkuri na karshe da aka yi a 2012ya janyo zanga-zangar gama-gari.

Yan Najeriya da dama da suke cikin kalubale da suka saba ganin yan siyasa na sama da fadi da arzikin kasar, suna ganin samar da man fetur a farashi mai sauki shi ne hanyar da za su amfana daga arzikin kasar.

Sai dai Tinubu ya sha nanata cewa ya zama dole a janye tallafin mai kuma makusantansa sun dage cewa yana da kudirin yin hakan.

"Yana da ikon tattaunawa da tuntuba kafin ya yanke mataki mai tsauri," Ministan gidaje Babatunde Fashola, wani makusancinsa wanda ya gaji gwamnatin Legas daga Tinubu a 2007, ne ya shaida wa BBC hakan.

Wani bangare da watakila zai iya dubawa domin rage radadin janye tallafin shi ne ya tallafa tare da inganta sufuri - wani abu da yake da kwarewa akai bayan da ya aiwatar da gagarumin tsarin sufuri a Legas da ya saukaka cunkoson ababen hawa.

Gwamnati mai barin gado ita ma ta nemi bashin dala miliyan 800 daga Bankin Duniya da nufin inganta shirin tallafa wa yan Najeriyar da janye tallafin zai fi shafa. Sai dai dole ne sai yan majalisar dokoki sun amince da bukatar - kuma har yanzu tana kasa tana dabo.

Rashin samun cikakken goyon baya

Kashi 37 cikin 100 na masu zabe ne kawai suka zabi Tinubu, wanda hakan ya sa ya zama zababben shugaban Najeriya da yake da mafi karancin kuri'u tun 1999.

Ya yi nasara a zaben mai zafi wanda ya fito da rarrabuwar kai ta fuskar addini da kabilanci a fili.

Dole ne ya zama ya yi aiki wajen daidaita al'amura game da zabin 'yan majalisarsa domin dinke barakar da aka samu.

Akwai alamu da ke nuna cewar ya soma yin hakan inda rahotanni ke cewa ya gana da yan siyasa biyu daga bangaren hamayya tun bayan da ya lashe zaben na watan Fabarairu.

Rabiu Musa Kwankwaso, babban abokin hamayyarsa daga arewacin Najeriya wanda kuma ya zo na hudu a zaben da aka yi.

Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers mai barin gado kuma mai karfin fada aji.

A matsayin gwamnan Legas, watakila Tinubu a iya cewa shi ne yake da mutane daga kabilu daban daban cikin jerin yan majalisarsa inda ya nada mutanen da ba yan asalin Legas ba kan mukamai muhimmai, wanda har yanzu, ba kasafai ake samun haka ba.

"Ya fi son yin aiki da kwararru masu nazari da bincike," in ji abokinsa Seye Oyetade da yake magana da BBC.

Amma yan siyasa, da bukatarsu ta zo daya, watakila za su fi saurin a shawo kansu fiye da miliyoyin matasan Najeriya da ba su zabe shi ba - musamman wadanda suka goyi bayan takarar Peter Obi na Jam'iyyar Labour.

Galibinsu na ganin an yi murdiya a zaben, duk da cewa hukumar zabe ta musanta hakan - kuma har yanzu karar da ke kalubalantar nasarar Tinubu na gaban kotu.

Makusantansa sun ce samar da ayyukan yi da kuma janyo matasa a harkar shugabanci, watakila Tinubu ya iya karkato da hankalinsu gare shi.

"Za ku ga gwamnati da za ta rungumi sabbin batutuwa da fasaha sannan za a ga matasa da dama a kusa da shi," in ji Fashola.

Saita tattalin arzikin kasa

Akasarin mutane sun amince cewa a matsayinsa na kwararren akanta, wani fanni da Tinubu ya kware a kai - amma abubuwa ba su taba yi wa 'yan Najeriya muni ba:

Mutum daya cikin uku ba su da aikin yi.

Hauhawar farashin kayayyaki ta kai kashi 22 cikin 100.

Mutum miliyan 96 ba sa iya kashe dala 1.90 kowace rana.

Yawan arzikin da Najeriya ke samarwa ya kai dala 2,065 a 2021 idan aka kwatanta da dala 70,248 a Amurka da dala 46,510 a Birtaniya.

Karancin kudaden shiga sakamakon faduwar farashin mai.

Mista Oyetade ya ce alkaluman sun banbanta sosai da abin da ya tarar a Legas cikin 1999.

Wannan na iya zama an kambama amma yadda Tinubu ya yi amfani da fasaha wajen inganta haraji a Legas da habaka kudaden shiga da fiye da kashi 400 cikin 100 a shekara takwas.

Ya sha yin magana game da burinsa na fadada haraji amma watakila wannan ya fi wahalar aiwatarwa a mataki na kasa la'akari da hauhawar farashi da karuwar talauci da matsalar tsaro da ke yawan hana mutane aiki.

Tinubu kuma yana fifita tsarin kamfanoni masu zaman kansu sabanin wanda zai gada Muhammadu Buhari wanda shi kuma ya mayar da hankali wajen inganta walwalar al'umma.

Amma alakarsu da Godwin Emefiele, gwamnan babban banki, wannan wani abu ne muhimmi.

Shugaban kasar mai jiran gado ya soki tsarin bankin na yawan amfani da musayar kudi da yawa.

Wannan ya sa darajar takardar naira ta yi tsada - ana sauya naira 460 kan kowace dala daya, ga mutane daban-daban da sai sun nema sun kuma jira kafin su samu.

Duk wani da ke son canja kudi dole ne ya yi amfani da kasuwar bayan fage da a yanzu ake sayar da naira kan 760 kan duk dala daya, hakan na nufin akwai gibi sosai tsakanin farashin hukuma da kuma na kasuwar bayan fage.

Dole ne Tinubu ya yi aiki da Emefiele wanda yake da sauran shekara daya a matsayin gwamnan bankin, matukar yana son a sake nazari kan tsarin.

Mutanen biyu sun samu baraka a alakarsu sakamakon matakin babban bankin na sake fasalin kudin kasar - lamarin da ya haifar da karancin takardun kudi - gab da lokacin zabe. An yi wa wannan tsarin kallon wani mataki na hana jam'iyya mai mulki damar lashe zabe - zargin da Emefiele ya karyata.

Garkuwa da mutane da matsalar tsaro

Tinubu zai so kamo bakin zaren wannan matsala cikin sauri, la'akari da girman matsalar. Gwamnatinsa za ta tunkari yan bindiga a arewa maso yamma da matsalar sace-sacen mutane a fadin kasar da rikicin kungiyar da ke neman ballewa daga kasar da ke kudu maso gabas. Da munanan rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma da ke ci gaba da gudana a jihohin da ke tsakiyar kasar.

A lokacin yakin zabe, mataimakin Tinubu, Kashi Shettima da ke jiran gado, ya ce zai yi amfani da kwarewarsa a matsayin gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabas mai fama da rikicin yan bindiga da Boko Haram.

Amma kalubalen tsaro sun sake dawowa tun bayan da bar ofis a 2019 sannan Shugaba Buhari, tsohon janar na soja, ya gaza samar da maslaha a tsawon shekara takwas da ya yi kan mulki - a maimakon haka, matsalar tsaron ta ta'azzara a fadin kasar.

Manufar Tinubu da Shettima ta hada da yakar ayyukan ta'addanci inda sojoji na musamman za su fatattaki masu garkuwa da masu tsattsauran ra'ayi.

Mafi muhimmanci shi ne, sun bayar da shawarar janye jami'an yan sanda daga zama dogaran fitattun mutane lamarin da zai sa a ga karin yan sanda kan tituna don yakar laifuka.

Kokarin kula da lafiya da sauran batutuwa

Yan hamayya sun ce shugaban mai jiran gado ya rasa kuzarin da ya yi amfani da shi wajen zamanantar da Legas.

Tun bayan zaben, ya yi bulaguro zuwa kasar waje sau biyu, abin da ya janyo tambayoyi game da lafiyarsa. A 2021, ya shafe watanni a London ana kula da lafiyarsa sai dai ba a bayyana cutar da ke damunsa ba.

Ya yi watsi da sukar da ake inda ya ce aikin na shugaban kasa ba ya bukatar lafiyar mai wasan tsere kuma makusantansa sun shaida wa mutane cewa Shugaban Amurka, Joe Biden ya fi shi shekaru - 80.

Amma yan Najeriya sun gaji da ganin yadda shugabanni suke shafe lokaci a kasashen waje don kula da lafiya lamarin da ya sa gwamnati ke rikici kan madafun iko. Wannan ya faru a karkashn Buhari da Umaru Musa Yar'adua wanda ya rasu a 2010.

Sun kuma damu da irin cece-kucen da ke biyo baya. Kafin a yi zabe, Tinubu ya musanta zarge-zargen alakarsa da miyagun kwayoyi da rashawa.

Tun nasararsa, an bankado cewa ya taba rike takardar fasfo din Guinea wanda bai saba doka ba amma dai ba a taba bayyana haka a baya ba.

Yayin da wani binciken Bloomberg ya ce dansa ya mallaki makeken gida a London da darajarsa ta kai fam miliyan 11. Tinubu da dansa ko ma na kusa da shi ba su ce komai game da rahoton ba sannan ba a tabbatar ba ko Tinubu yana da hannu wajen sayen gidan.

Makusantan Tinubu za su damu cewa zurfafa bincike ka iya karkatar da hankalinsa daga muhimmin nauyin da ke shirin rataya a wuyansa.

Source: BBC