BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Duniya na cikin barazanar fuskantar yanayin zafi mafi tsanani a 2024, in ji masana

Hoton alama

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Wani abu na sauyin yanayi da aka fi sani da El Niño ya fara bayyana a tekun Pacific, kuma watakila ya kara zafi a duniyar da ke dumuma sakamakon sauyin yanayi.

Masana kimiyyar Amurka sun tabbatar da cewa El Niño ya fara bayyana.

Masanan sun ce da alama zai sa shekarar 2024 ta zama shekara mafi zafi a duniya.

Suna fargabar cewa hakan zai sa duniya ta wuce maki 1.5 na maunin celcius da aka kayyaɗe mata.

Haka kuma wannan zai shafi yanayin duniya ta hanyar kawo fari a Austiraliya da karin ruwan sama a Amurka tare da raunana damina a kasar Indiya.

Watakila yanayin ya ci gaba har zuwa karshen bazara kuma bayan haka ne tasirinsa zai ragu.

Masu bincike sun shafe tsawon watanni suna nuna kwarin gwiwa kan aukuwar sauyin yanayin El Niño a tekun Pacific.

"Yanzu yana kara ta'azaara, akwai alamu a hasashen da mu ka yi na tsawon watanni da dama amma da alama zai kai kololuwa a karshen bana ta fuskar karfi", In ji Adam Scaife babban jami'i a hukumar hasashen yanayi ta Birtaniya.

"Da alama za a yi zafi mai tsanani da ba a taba ganin irinsa ba a badi. Ya dogara ne da yadda girman El Niño zai kasance- amma ana ganin zai kasance mai girma a karshen badin, kuma wannan ya nuna cewa za a yi zafin da ba a taba ganin irinsa ba a badi".

Shi dai yanayin El Niño yana da matakai uku wato, zafi da sanyi da kuma tsaka-tsaki.

Yanayin zafi na El Niño yana faruwa a kowace shekara biyu zuwa bakwai kuma ana ganin ruwa mai dumi yana zuwa saman tekun Kudancin Amurka kuma yana bazuwa cikin teku inda yana tura zafi mai yawa zuwa sararin samaniya.

Shekarun da aka yi zafi mai tsanani sun haɗa da 2016 wadda ita ce shekarar da aka fi zafi da ba a taba ganin irinsa ba kuma wannan ya faru ne bayan shekara ɗaya da faruwar El Niño.

Cibiyoyin hasashen yanayi na duniya na amfani da dubaru daban -daban wajen yanke shawara a kan lokacin da al'amarin zai faru.

Masana kimiya a Amurka na sa ido ne a kan tekun idan ya kai maunin celcius na 0.5 na zafi fiye da wata guda, kuma dole ne zafin ya yi tasiri akan yanayi kuma dole a samu shaida da ke nuna cewa al'amarin na ci gaba da ta'azara.

Wadannan dai abubuwa ne da suka faru a watan Mayun da ya gabata.

A cikin sanarwa da hukumar kula da teku da yanayi ta Amurka ta fitar ta ce alamomin "El Niño sun fara bayyana".

Masu binciken sun ce duk da cewa yanayin zai yi tasiri ne na watanni kalilan amma zai shafi kasashen duniya baki-ɗaya.

Masu binciken suna tsammanin za a fuskanci matsaloli da suka haɗa da rashin ruwa a Austiraliya da wasu sassan Asiya tare da ruwa sama a lokacin hunturu a Amurka da kuma fari a Afrika.

Kamar yadda aka saba gani a baya, matsalar za ta shafi mutane da dama kuma za ta sa a kashe makuɗan kuɗi.

Sauyin yanayin na El Niño da ya faru a 1997 zuwa 1998 ya sa an kashe kuɗi fiye da dala tiriliyan 5, inda mutane 23,000 suka rasa rayukansu sanadin mahaukaciyyar guguwa da ambaliyar ruwa.

Haka kuma akwai yuwuwar cewa sigar ta bana za ta sa ta zarce ta 2016 a matsayin shekarar da ta fi zafi a duniya.

Source: BBC