Menu

Ƙasashen da aka samu dawowar juyin mulki baya-bayan nan a Afirka

Sojojin Nijar da suka juya mulki

Fri, 28 Jul 2023 Source: BBC

Majalisar Ɗinkin Duniya ta dakatar da ayyukan jin ƙan ɗan'adam a Nijar, bayan hamɓaras da Shugaba Mohamed Bazoum a wani juyin mulkin sojoji ranar Laraba.

Mai magana da yawun Majalisar Ɗinkin Duniya Stephane Dujarric ya ce ayyukan ba da agajin jin ƙai a Nijar "an jingine su, bisa la'akari da halin da ake ciki".

Ofishin Ayyukan Jin Ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙiyasin cewa 'yan Nijar aƙalla miliyan 4.3 ne a yanzu ke buƙatar agaji, fiye da kashi biyu na mutum miliyan 1.9 da suka buƙaci tallafi a 2017.

Wata sanarwar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce adadin mutanen da ke fama da matsanancin rashin abinci, mai yiwuwa zai ƙaru zuwa miliyan uku a tsakiyar damuna tsakanin watan Yuni zuwa Agusta kafin a yi girbi.

A ɓangare guda, Mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris ta yi Allah-wadai da duk wani yunƙuri na ƙwace mulki ta hanyar amfani da ƙarfi a Nijar, inda ta bayyana tsananin damuwa game da juyin mulkin da ya faru lokacin da take zantawa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu.

Wata sanarwa da fadar White House ta fitar ta ambato Kamala Harris na cewa duk wasu muhimman ayyukan haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Nijar, an gina su ne bisa doron cewa sai Nijar ta ci gaba da mutunta ƙa'idojin dimokraɗiyya.

Ana ci gaba da tsare Mohamed Bazoum a fadar shugaban ƙasa kuma babu masaniya ƙarara a kan ko wane ne yake iko da ƙasar, bayan sojoji a ranar Laraba sun yi shelar karɓe iko.

Faransa, tsohuwar uwargijiyar Nijar da Amurka sun yi kira a saki Bazoum cikin gaggawa kuma a mayar da ƙasar kan turbar amfani da tsarin mulki.

Ƙwace ikon sojojin a Nijar shi ne juyin mulki ko yunƙurin ƙwace mulki karo na tara cikin shekara uku a Afirka ta Yamma da Afirka ta Tsakiya, wani yanki da ya yi namijin ƙoƙari a cikin shekara goma wajen kakkaɓe ƙaurin sunan da ya yi a matsayin "sashen da juyin mulki ya yi katutu", kafin taɓarɓarewar tsaro da cin hanci da rashawa su sake buɗe ƙofa ga sojoji.

Ga jerin ƙasashen da aka yi juyin mulki a shekarun baya-bayan nan

Burkina Faso

Rundunar sojojin Burkina Faso ta hamɓarar da Shugaba Roch Kabore a watan Janairun 2022, inda suka zarge shi da gaza shawo kan tarzomar masu iƙirarin jihadi.

Jagoran masu juyin mulkin Laftanal Kanal Paul-Henri Damiba ya yi alƙawarin dawo da tsaro a ƙasar, sai dai hare-hare sun daɗa ƙazancewa, abin da ya zaizaye ƙwarin gwiwar dakarun tsaro inda aka samu juyin mulkin a karo na biyu wata takwas bayan na farko.

Jagoran sojoji masu juyin mulki Kaftin Ibrahim Traore ne ya ƙwace iko a watan Satumba bayan wani boren sojoji.

Mali

Wani rukunin sojoji masu muƙamin kanal-kanal ƙarƙashin jagorancin Assimi Goita ne suka hamɓare Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan 2020.

Juyin mulkin ya zo ne bayan jerin zanga-zangar ƙin jinin gwamnati game da taɓarɓarewar tsaro da taƙaddama kan sakamakon zaɓen 'yan majalisa da kuma zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Matsin lamba daga maƙwabtan Mali na Afirka ta Yamma, ya tilasta wa sojoji amincewa su miƙa mulki ga wata gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin jagorancin fararen hula inda aka damƙa mata alhakin kula da wani shirin miƙa mulki na wata 18 ga zaɓaɓɓun shugabanni bisa doron dimokraɗiyya a watan Fabrairun 2022.

Sai dai shugabannin juyin mulkin sun yi rikici da shugaban riƙon ƙwaryar, Kanal Bah Ndaw mai ritaya, inda suka kitsa wani juyin mulkin karo na biyu a watan Mayun 2021.

Asimi Goita wanda ya riƙe muƙamin mataimakin shugaban riƙon ƙwarya, ya sake ɗarewa kan karagar shugabancin ƙasar.

Ƙungiyar Ecowas ta ɗage wasu takunkumai da ta sanya wa Mali bayan shugabannin sojin sun gabatar da ƙudurin shirin miƙa mulki na shekara biyu zuwa hannun gwamnatin dimokraɗiyya tare da wallafa wata sabuwar dokar zaɓe.

An tsara cewa ƙasar za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a watan Fabrairun 2024, don komawa ƙarƙashin tsarin mulki.

Chadi

Rundunar sojin ƙasar Chadi ta ƙwace mulki a watan Afrilun 202,1 bayan kashe Shugaba Idriss Deby a fagen yaƙi lokacin da ya ziyarci dakarunsa da ke gwabza faɗa da 'yan gawaye a arewacin ƙasar.

A ƙarƙashin dokokin Chadi, shugaban majalisar dokoki ne ya kamata ya zama shugaban ƙasa.

Sai dai wata majalisar sojoji ta wuce gaba, inda ta rusa majalisar dokokin, da sunan tabbatar da daidaituwar al'uamura da kwanciyar hankali.

Daga nan sai aka bayyana Janar Mahamat Idriss Deby, ɗan marigayi Idriss Deby a matsayin shugaban riƙon ƙwarya kuma aka ɗora masa alhakin gudanar da shirin miƙa mulki tsawon wata 18 ta hanyar yin zaɓuka.

Musayar ikon wanda ya saɓa da tsarin mulki ya janyo yamutsi a N'Djamena, babban birnin ƙasar, kafin sojoji su kwantar da shi daga bisa.

Guinea

Kwamandan dakaru na musamman Kanal Mamady Doumbouya ya kifar da Shugaba Alpha Conde a watan Satumban 2021.

Shekara ɗaya kafin nan, Conde ya canza tsarin mulki don ya kauce wa ƙa'idar da aka shimfiɗa wadda za ta hana shi sake tsayawa takara a karo na uku, abin da ya haddasa bore a sassa da dama.

Doumbouya ya zama shugaban riƙo, kuma ya yi alƙawarin gudanar da zaɓukan dimokraɗiyya a ƙarƙashin wani shirin miƙa mulki na shekara uku.

Ecowas ta yi watsi da jadawalin, inda ta ƙaƙaba takunkumai a kan shugabannin mulkin sojan tare da iyalansu ciki har da rufe asusun ajiyar bankunansu.

Daga nan ne kuma gwamnatin mulkin sojan ta sake gabatar da wani shirin miƙa mulki na wata 24, farawa daga watan Janairun 2023, sai dai jam'iyyun adawa sun ce sojoji ba su yi wani abin a-zo-a-gani ba wajen kafa cibiyoyi da jadawalin mayar da ƙasar kan turbar amfani da tsarin mulki.

Source: BBC