BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ƙasashen musulmi sun fusata da kona Alƙur'ani a Sweden

An kone Alkur'ni a ranar baban sallah

Fri, 30 Jun 2023 Source: BBC

Kasashen musulmi na duniya na ci gaba da yin Allah wadai da kona Alƙur'ani da masu zanga-zanga suka yi a kasar Sweden.

Kasar Maroko ta yi wa jakadanta na can kiranye, sakamakon lamarin da ya faru a birnin Stockholm.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar a birnin Rabat ta kira matakin a matsayin rashin da'a ga al'ummar musulmi, yayin da suke bikin Babbar Sallah.

Ministan harkokin wajen Turkiyya ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya ce wadanda suka shiya zanga-zangar na da hannu a abun da ya faru.

Yanz haka ana bincikar wanda ya shirya zanga-zangar da aka ce dan Iraqi kan zargin tunzura jama'a.

Wata kotu a Sweden ce ta yanke hukuncin a kyale masu zanga-zangar su yi gudanar da ita, bisa hujjar 'yancin fadar albarkacin baki.

Ba dai wannan ne karon farko da aka taba samun wani abu makamancin haka ba a Sweden.

Lokaci zuwa lokaci akan yi zanga-zanga irin wannan, inda jama'a ke taruwa suna kona littafin mai tsarki na musulmi.

A kasashen duniya da dama ana gudanar da zanga-zanga da kona tutar kasar don nuna damuwa kan abun da ya faru.

Source: BBC