Menu

‘Yan bindiga sun hana mu girbe amfanin gona‘

Terrorists New 1 Yan bindiga sun addabe yan Najeriya musamma a arewacin kasa

Sun, 17 Dec 2023 Source: BBC

Al’ummar garuruwan Dantsuntsu da Nahuta a yankin karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina da ke arewa maso yamamcin Najeriya sun koka kan yadda hare haren ‘yan bindiga ke hana su girbe amfanin gona.

Mazauna wadannan garuruwan sun ce duk wanda ke zaune cikin wadannan garuruwan da ma kewayensu na cikin zaman dar dar saboda babu tabbacin cewa za a kai hari ko kuma a‘a.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC cewa hari na baya bayan nan da aka kai musu shi ne wanda mutane suka tafi gona don girbe amfanin gonarsu sai kawai ba su yi aune ba suka ga 'yan bindiga sun zagaye su kuma nan take suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ya ce,“ A nan aka kashe mutum hudu aka yi awon gaba da wasu sannan kuma a yanzu haka ana neman mutum takwas“.

Ya kara da cewa ba su debi komai ba ban da mutanen da suka dauka da kuma wadanda suka kashe.

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar harin inda kakakin rundunar ya ce mutum hudu aka kashe da kuma mutum takwas da aka yi awon gaba da su ba a gani ba a harin.

Ya ce tuni aka aika da jami'an ƴan sanda yankin domin kokarin kubutar da mutanen da aka sace.

Mazauni yankin ya ce harin ba shi ne na farko ba domin an saba kai ma su irin wannan hare haren.

Mazaunin yankin ya ce duk da yake akwai jami’an tsaro amma ba lamarin ya yi kamari.

“A wannan yankinna Batsari, ‘yan bindiga sun taba yi mana kulle na hana zuwa gona tsawon wata guda gashi lokacin ake noma har sai da abin amfanin gona ya lalace”.

”Da noma muka dogara amma ‘yan bindigar nan sun hana mu mu yi noma, gashi yanzu kuma dan abin da muka samu muka noma sun hana mu mu girba, in ji shi.

Mazaunin yankin ya ce suna da albarkatun noma amma saboda tashin hankali da zaman dar dar a kan hare haren ‘yan bindiga yanzu an gurgunta su har ta kai abin da mutum ma zai ci na nema ya yi masa wuya.

Yankin na Batsari da ke jihar Katsina dai na daga yankunan da ke fama hare haren ‘yan bindiga wanda hakan ke ci gaba da kassara sha’anin zamantakewa da tattalin arziki yankin da ma jihar baki daya.

Matsalar hare haren ‘yan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya dai na ci gaba da zama abin damuwa a yayin da gwamnati a na ta bangaren kuma ke cewa tana kokari domin magance matsalar.

Source: BBC