BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

 'Duk masu kudin garinmu sun yi hijira saboda rashin tsaro'

Nigeria Flags Tutar Najeriya

Wed, 12 Oct 2022 Source: BBC

Wannan labari yana cikin jerin labaran da BBC Hausa za ta gabatar bayan neman jin ra'ayoyin ƴan Najeriya a manyan fannonin da suka fi shafi 'yan kasar. Wannan shiri ne na musamman da BBC ta tsara dangane da shirin manyan zaɓukan da ƙasar za ta gudanar daga watan Fabrairun 2023. Fannonin da za a yi duba a kai din su ne na tsaro da ilimi da tattalin arziki da lafiya da kuma cin hanci. Daruruwan mutane ne suka aiko da labaransu, kuma za mu wallafa 25 ne kawai, ɗaya a kowace rana daga 10 ga Oktoban 2022. Al'umar jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar sassa da dama na jihar sakamakon ayyukan 'yan bindiga, wadanda ke cin karensu babu babbaka a yankin. Jihar Katsina dai na fama da tashe-tashen hankula daga ayyukan 'yan bindiga a 'yan shekarun baya-bayan nan, inda ake samun rahotonnin kai hare-hare a makarantu tare da sace dalibai masu yawa a makarantar sakandire ta Kankara. Ga kuma rahotonin sace matafiya a kan titunan jihar, da hare-hare a kan kauyuka da dama na jihar tare da sace mutane domin neman kudin fansa, da dai sauran matsaloli masu yawa, da ke ci wa alu'umar jihar tuwo a ƙwarya sakamakon ayyukan 'yan bindiga. Matsalolin da rashin tsaro ya haifar wa KatsinaAkwai tarin matsaloli masu dimbin yawa da rashin tsaro ya haifar wa jihar Katsina, kama wasu matsalolin za su dade suna yi wa cigaban jihar tarnaki, domin kuwa za a dauki lokaci mai yawa kafin a shawo kansu Gudun hijira Matsalar rashin tsaro ta tilasta wa mutane da dama yin gudun hijira daga wasu sassa na jihar zuwa cikin babban birnin jihar ko ma wasu makwabtan jihohi, kamar yadda wani mazaunin jihar mai suna Abdallah Ismail Gwarjo da ke yankin karamar hukumar Matazu a jihar ya shaida wa BBC Ya ce ''A gaskiya matsalar tsaron da ke addabarmu ta ta'azzara, abin ya wuce duk inda ake tunani. "Mutanen da ke garin Gwarjo musamman masu hannu-da-shuni duk sun yi hijira sakamakon rashin tsaro. "Babu ranar da ba za ka ji an kashe ko an dauki mutum ba''. Haka shi ma wani mai suna Mubarak Funtua ya shaida wa BBC cewa matsalar tsaron ta sa suna neman wajen da za su tsuguna domin kuwa a cewarsa ''garinmu ya fi karfinmu yau su zo, gobe su zo. Ina za mu sa rayuwarmu''? Rufe makarantu Ayyukan 'yan bindiga sun tilasta rufe makarantu a wasu sassan jihar Katsina, bayan kai hari makarantar sakandiren Kankara tare da sace dalibai masu yawa, inda gwamnatin jihar ta rufe makarantun sakandire da na firamare zuwa wasu watanni kafin daga bisani a sake bude su. Ibrahim Khalil wani mazaunin jihar ya ce ''matsalar rashin tsaro a jihar katsina tana shafarmu ne ta hanyar rashin zuwa karatu a makaratun Firamare da sakandire, ta hana yaranmu zuwa makaranta domin samun Illimi''. Hana cin kasuwanni Haka kuma rashin tsaron ya tilasta rufe kasuwanni da dama a fadin jihar, sakamakon sace mutane da 'yan bindiga ke yi a kan hanyarsu ta zuwa kasuwanni, ko yadda suke kai hari cikin kasuwannin jihar domin sace kayan abinci da kayan amfanin yau-da-kullum. ''Matsalar rashin tsaro a jihar katsina tana shafarmu ne a lokacin zuwa kasuwani, ta hana al’umma zuwa wasu kasuwanni domin gudanar da harkokin kasuwanci'', in ji Ibrahim Khalil. Rashin nomaWata babbar matsala da ayyaukan 'yan bindiga suka haddasa a jihar Katsina da ma wasu sassan arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, ita ce hana manoma zuwa gonakinsu domin yin noma. Wani abu da ke kara ta'azzara tsada tare da karancin abinci tsakanin al'umma. A wasu yankunan kasar 'yan bindigar kan karbi kudade masu yawa daga hannun manoman kafin su bar su, su je gonakinsu domin yin noma. Ibrahim Khalil ya ce ''Matsalar ta hana al’uma zuwa gonakinsu domin yin noma, a takaice in ce matsalar tsaro ta hana al’uma gudanar da al’amuransu na yau da kulum da suka saba gudanarwa'' ''Sakamakon yadda yan bindiga ke yi mana cin kashi a kauyukanmu ya sa noma ya ki yiwuwa muna bukatar taimako na abinci'', in ji Mubarak Funtua wani mazaunin jihar. Zaman firgici da tsoro a zukatan al'umma Wani abu shi ma da matsalar tsaro ya haifar a jihar shi ne zaman firgici tsakanin al'umma, da rashin nutsuwa. Kasancewar a kowanne lokaci za a iya kawo hari tare da sace mutane ya sa mutane na zaune cikin firgici. Mubarak Funtua ya ce ''Na kasance a cikin matsanancin hali sakamakon yadda ƴan bindiga ke yi mana cin kashi a kauyakunmu, yau su zo gobe su zo ina za mu sa rayuwarmu''?

Source: BBC