BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Ƙungiyoyin Saudiyya na son Salah da Mbappe, Arsenal na dab da karɓo Toney

68477854 Mohamed Salah

Sun, 17 Dec 2023 Source: BBC

Kungiyoyin Saudiyya na son karbo dan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah mai shekara 31 a bazara. (Mail)

Dan wasan Portugal Fabio Carvalho zai iya komawa Fulham idan Liverpool za ta kira dan wasan mai shekara 21 daga aro a RB Leipzig. (Mirror)

Dan wasan gaba na Brentford da Ingila Ivan Toney, mai shekara 27, rahotanni sun yana dab da komawa Arsenal. (Fabrizio Romano via Mail)

Daraktan Lig din Saudiya Michael Emenalo ya ce suna tattaunawa kan kokarin karbo dan wasan Paris St-Germain da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24. (Marca - in Spanish)

Chelsea da Manchester City da Barcelona na farautar matashin dan wasan River Plate da Argentina mai shekara Claudio Echeverri. (Mirror)

Kungiyoyin Premier da suka kunshi Liverpool da Arsenal da Chelsea, rahotanni sun ce suna sa ido kan dan wasan gaba na Sunderland Jobe Bellingham, mai shekara 18. (Ekrem Konur)

Eintracht Frankfurt na da zabin sayen dan wasan Manchester United Donny van de Beek, mai shekara 26, kan kasa da fam miliyan 10. (Sky Germany via Florian Plettenberg)

AC Milan ta tuntunbi Barcelona kan dan wasanta na baya mai shekara 28 Clement Lenglet da ke matsayin dan wasan aro Aston Villa. (Caughtoffside)

Manchester City na son Everton ta biya fam miliyan 7.5 kan dan wasan tsakiya na Ingila Kalvin Phillips. (Football Insider)

Barcelona na farautar matashin dan wasan Djurgarden Lucas Bergvall mai shekara 17. (Football Transfers)

Source: BBC