BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Gwamnati ta gaza kare ma'aikata daga tasirin ƙirƙirarriyar basira ta AI'

Hoton alama

Wed, 19 Apr 2023 Source: BBC

Ƙungiyar ƙwadago ta TUC tana kira da a ɗauki tsatstsauran mataki domin kare ma'aikata daga amfani da bayanan da aka samo daga ƙirƙirarriyar basira wato Artificail Intelligence Systems.

Fasashohin AI a yanzu suna yanke shawara mai haɗari da sauyin rayuwa game da rayuwar ma'aikata ciki har da kula da ma'aikata da ɗaukar su da kora da kuma ɗiban ma'aikata, in ji ƙungiyar da ke wakiltar ma'aikata.

Amma wata sabuwar doka za ta sirka kariyar da ake da shi, in ji ta.

Gwamnati ta ce tunanin TUC ba daidai bane kuma matakan kariya za su ci gaba da aiki.

Wani kakaki ya ce sun duƙufa wajen ingantawa da kuma tabbatar da ƴancin ma'aikata: "An tsara ƙirƙirarriyar basira ne domin samar da ci gaba da samar da sabbin ayyukan yi masu gwaɓi a faɗin Birtaniya yayin da kuma za a bamu damar aiwatar da ayyukanmu cikin inganci da aminci.

"Shi ya sa muke aiki tare da kamfanoni da hukumomi domin tabbatar da cewa ana amfani da fasahar AI yadda ya kamata a harkokin kasuwanci."

AI wani reshe ne na ilimin kimiyyar fasaha da ke ƙirƙirar na'urori da manhajoji da ke aiwatar da ayyukan da ke buƙatar mutane su aiwatar da su, misali, yanke shawara ko kuma gane magana.

Masu bincike da dama sun bayyana damuwa game da amfani da ƙirƙirarriyar basirar a wuraren aiki musamman wajen ɗaukar ma'aikata da ake amfani da wasu na'urori masu tantance cancantar mai neman aiki. Sun yi bayani cewa fasashohin ba su da tushe a ɓangaren kimiyya kuma suna tare da son ra'ayi.

TUC ta ce ana amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen nazarin saƙonnin fuska da yanayin murya da kuma magana domin tantance ko mutum ya cancanta ya samu aiki.

Idan aka ƙyale abin ba tare da dubawa ba, AI na iya haifar da wariya sosai a wajen aiki. Misali, na'urorin da ake amfani da su wajen tantance saƙonnin fuska na iya zama naƙasu ga mai neman aiki ko ma'aikata da ke da buƙata ta musamman.

Sai dai wasu kamfanonin da ke tallata fasahar AI na jayayya cewa kwamfutoci za su yanke shawara ba tare da son rai ba idan ka kwatanta da shawarar da bil adama zai ɗauka.

Mary Towers, wata jami'ar kare haƙƙin ma'aikata a TUC ta faɗa wa BBC cewa bincikensu ya gano ana amfani da fasahohin AI a masana'antu da dama" a matakin ɗiban ma'aikata kamar wajen tantance kundin bayanin mai neman aiki da tsarin aiki da matakan ladabtarwa da ƴanci da kuma batun korar ma'aikaci".

"Mun gano shaidar ana amfani da fasashohin AI ta hanyoyi da dama da za ka yi tsammanin mutum ne ya aiwatar da ayyuka a wajen aiki," in ji ta.

'Burin da ba za a iya cimma ba'

Ana iya amfani da fasashohin AI wajen bibiyar ƙwazon ma'aikata , wani lokacin yana ɗaukan mataki na sallamar ma'aikata ta na'ura.

TUC ta yi gargaɗi cewa ana iya amfani da fasahar AI wajen tsara burin da ba za a iya cimma ba da zai iya jefa ma'aikata cikin haɗari da zai yi mummunan tasiri kan lafiyarsu".

Wasu kamfanoni na buƙatar ma'aikata su ɗauki wasu na'urori da ke naɗar bayanai game da ayyukansu wanda za a iya nazari a kai. Wani ma'aikaci ya faɗa wa masu tallata manufofin AI cewa hakan na nufin idan suka tashi zuwa banɗaki a lokuta da dama, na'urar za ta ankarar kuma za su yi bayanin dalilin da ya sa ba sa aiki.

A watan da ya gabata ne, gwamnati ta wallafa wani rahoto kan fasahar AI wanda ya bayar da shawara kan yaɗa ƙa'idojin fasahar a maimakon samar da sabuwar hanya ta ibiyar ma'aikata.

A cewar TUC, rahoton bai bayar da gamsassun ƙa'idoji ga hukumomi ba kan yadda za a tabbatar da yin amfani da Ai yadda ya kamata a wajen aiki.

Ya kuma bayar da shawara ƙudirin kare bayanai da bayanan fasaha da aka yi wa zama na biyu a ranar Litinin, zai warware kariya da dama cikin dokar kare bayanai - har da ikon ɗan adama ya yi bitar shawarar da fasaha ta yanke.

'Nazarin ɗan adam'

TUC na neman kamfanoni su bayyana yadda ake amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen yanke shawara game da ma'aikata. Ya kamata dukkan shawarwarin su bi ta nazarin ɗan adam don ma'aikata na iya ƙalubalantarsu, in ji ƙungiyar.

Gwamnati na ganin tsare-tsarenta ba su ci karo da ƴancin ma'aikata na neman nazarin ɗan adam kan shawarwarin da na'ura ta yanke.

Ƙudirin zai ci gaba da tabbatar da kariyar da ma'aikatan Birtaniya ke da ita a yanzu yayin bai wa ƙungiyoyi dama, in ji TUC.

Sai dai wasu ƙungiyoyin suma sun soki ƙudirin. Ƙungiyar Connected by Data ta faɗa wa BBC cewa: "Ƙudirin zai rage damar ma'aikata ta samun bayanai game da su ko kuma su ƙalubalanci yadda aka yi amfani da su, hakan na nufin wataƙila ba za su taɓa sanin abin da ya sa damarsu ta aiki take cikin ƙalubalke ba."

Domin nuna dalilin da ya sa irin waɗannan ƙa'idojin ke da muhimmanci, akwai wata ƙara da ke gaban kotu wadda ta umarci wasu kamfanoni biyu su soke bayanan da ke da alaƙa da matakan da na'ura ta yanke na korar ma'aikata a Birtaniya da Portugal.

Angela Rayner, mataimakiyar shugaban masu rinjaye na Jam'iyyar Labour ta goyi bayan kiran da TUC ta yi, inda ta faɗa wa BBC cewa "tuni fasahar AI ta fara sauya tattalin arzikin ƙasar".

Dole ma'aikata su kasance suna da ra'ayi kan yadda ake aiwatar da fasahohi", in ji ta.

"Labour za ta inganta haƙƙoƙin aiki da kariya don su dace da tattalin arzikin zamani."

Source: BBC
Related Articles: