Hukumar kwallon ƙafa ta Afrika ta fitar da sunayen mutum uku da za su iya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka ta shekarar 2023.
Ɗan wasan Najeriya da Napoli Victor Osimhen da Achraf Hakimi na Morocco da PSG da kuma Mohammed Salah na Liverpool da Egypt ne suka yi ragowa zuwa matakin ƙarshe na gasar.
A ranar Alhamis 7 ga watan Disamba ne CAF ta bayyana sunayen nasu a shafinta na X, yayin da ya rage saura kwana huɗu a yi bikin a birnin Marrakech na Morocco.
Dan wasan Senegal Sadio Mane ne ke riƙe da kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka wanda ya lashe a 2022.
A ranar 11 ga watan Disamba wato ranar Litinin ne za a yi bikin a Morocco.
Za a bayar da irin wannan kyauta ga gwarzuwar ƙwallon ƙafa ta Afirka ta bana.
Akwai irin wannan dama da za a samu a fannin matasan 'yan wasa na nahiyar, sai kuma masu tsaron raga da masu horaswa da dai sauransu.
Asisat Oshoala (Nigeria, Barcelona)
Thembi Kgatlana (South Africa, Racing Louisville)
Barbara Banda (Zambia, Shanghai Shengli)
Mai horaswa na shekara
Abdelhak Benchika (Algeria, Simba SC)
Walid Regragui (Morocco)
Aliou Cisse (Senegal)
Mai horaswa ta shekara
Reynald Pedros (Morocco)
Desiree Ellis (South Africa)
Jerry Tshabalala (South Africa, Mamelodi Sundowns)
Mai tsaron raga na shekara
Andre Onana (Cameroon, Manchester United)
Mohamed El Shenawy (Egypt, Al Ahly)
Yassine Bounou (Morocco, Al Hilal)
Mai tsaron raga ta shekara
Khadija Er-Rmichi (Morocco, AS FAR)
Chiamaka Nnadozie (Nigeria, Paris FC)
Andile Dlamini (South Africa, Mamelodi Sundowns)
Matashin ɗan wasa na shekara
Abdessamad Ezzalzouli (Morocco, Real Betis)
Lamine Camara (Senegal, Metz)
Amara Diouf (Senegal, Metz)
Matashiyar 'yar wasa ta shekara
Comfort Yeboah (Ghana, Ampem Darkoa)
Nesryne El Chad (Morocco, Lille)
Deborah Abiodun (Nigeria, Pittsburgh Panthers)
Tawagar maza ta shekara
Gambia
Morocco
Senegal
Tawagar mata ta shekara
Morocco
Nigeria
South Africa
Ƙungiyar maza shekara
Al Ahly (Egypt)
Wydad Athletic Club (Morocco)
Mamelodi Sundowns (South Africa)
Ƙungiyar mata ta shekara
AS FAR (Morocco)
Sporting Casablanca (Morocco)
Mamelodi Sundowns (South Africa)