Duk da cewa tashin farashin kayayyaki a Najeriya bai kai ƙololuwa ba amma talakawa na matuƙar shan wahala a sakamakon haka.
BBC ta yi wani bincike game da yadda mutane da yawa ke gudanar da rayuwarsu a ƙasar da matsin tattalin arziƙin ta ke neman yi wa katutu.
Najeriya wadda ita ce ƙasa mafi girman tattalin arziƙi a Afrika na fuskantar tsadar rayuwa tun gabanin shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin mai a watan Mayu, abin da ya ƙara ta’azzara yanayin.
Ga wata matashiya ‘yar shekara 18 da ke zaune a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kullum da safe tana zagayawa gidaje daban-daban domin roƙo abin da za su karin kumallo da shi.
Sama da shekara guda ita da ‘yar uwatta ce ke samar da abincin da ake ci a gidansu da ake da yara shida, safe da rana da kuma dare.
“Ba haka rayuwarmu take ba a baya, waɗannan sauye-sauyen da aka samu ne suka shafe mu.
“Mahaifunmu sayar da kaya yake a kasuwar kwari gabanin abubuwa su taɓarɓare masa ya zama ko abinci bai iya saya mana.”
Ta ce duka gidansu babu mai zuwa makaranta, babban abin da yake gabansu a yanzu shi ne yadda za su tsira daga yunwa.
Gidaje da dama a Najeriya na cikin irin wannan yanayi da gidansu matashiyar nan ke ciki, kuma mutane da yawa wannan labarin nata ba zai ba su mamaki ba saboda sabo da suka yi da yanayin da ake ciki.
Wani mutumi kuma ya fito a gidan wani radiyo a Kano, ya bayar da labarin yadda mutane ke karbar bashin garin tuwo domin dafawa a ci.
Kwanakin da suka gabata ne ƙungiyar masu biredi a ƙasar ta ce ta yi ƙarin kashi 15 cikin 100 na farashin biredin.
A cewar alƙaluman baya-bayan nan, an samu ƙarin farashin kayayyaki zuwa 22.79 daga 22.41 a watan Mayu, wannan ne wata na huɗu a jere da ake samun tashin farashin.
Hauhawar farashin ta fi shafar farashin abinci da hayar gida da ruwa da wuta da kuma man fetur.
Farashin kilo ɗin tumatiri da attaruhu da tattasai duka ya tashi, inda ake sayar da kilo biyu a naira 3,000 a cikin kasuwa.
Yayin da hauhawar farashin ke ƙara haɓɓaka sakamakon cire tallafin mai, a gefe guda kuma kayan abinci na ƙara tsada saboda tashin farashin dala.
Damuwar dai ita ce har yanzu gwamnati ba ta ce komai ba game da ƙarin albashin ma'aikata daga mafi ƙarancin albashi da ake da shi na naira 30,000.