Menu

'Yadda ƴan sanda su ka ci mutunci na' - Jikan Mandela

 118487043 4831f6fe 0c3b 43ea 98c4 59969fe2a217 Mandela ya ce cin zarafin ya auku ne ranar 8 ga watan Mayu

Fri, 14 May 2021 Source: BBC

Daya daga cikin jikokin tsohon shugaban Afirka ta Kudu marigayi Nelson Mandela ya ce zai kai karar 'yan sanda saboda mummunan cin zarafinsa da su ka yi.

Kafofin yada labarai na kasar sun ce Mayibuye Melisizwe Mandela ya sanar cewa 'yan sanda sun tsayar da shi tare da wasu mutum uku a kan hanyarsu ta komawa gida bayan ya kai wata ziyara zuwa gidan tarihi na Mqhekezweni Great Place - inda shi ne gidan da Mandela ya yi rayuwarsa tun yana karami.

Ya ce cin zarafin ya auku ne ranar 8 ga watan Mayu.

Mista Mayibuye ya kuma ce 'yan sandan sun nuna musu "keta" iri-iri, ciki har da dukansa da su ka yi a ka - wanda ya sa ya sami rauni a saman idonsa.

Ya kuma ce sun bukaci duba cikin motar da yake tafiya a ciki gabanin daukan matakin da su ka yi a kansa.

"Da su ka fara cewa mu kwanta a kasa, sai na ki amma na bukaci su caje ni yayin da nake tsaye a jikin mota ta, musamman ganin cewa ana ruwa alokacin kuma hanyar da mu ke kai ba ta da kwalta.

Mista Mandela ya nuna hotonsa wanda ya wallafa a Facebook bayan cin zarafin da aka yi ma sa:



Ya kuma shigar da kara a ofishin 'yan sanda na Madeira da ke lardin Eastern Cape, kuma 'yan sandan lardin sun ce suna sane da koken amma ba su kara cewa komai ba.

Source: BBC
Related Articles: